Rahotanni daga garin Maidabino a ƙaramar hukumar Ɗanmusa da ke jihar Katsina sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai mummunan harin wuce gona da iri tare da kashe mutum tara.
A daren jiya Asabar ne dai ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka dira ƙauyen Maidabino da misalin karfe 7:00 na dare har zuwa 2:30 suna barna da ta’asa.
- Atiku Ya Ziyarci Buhari Da Sarkin Daura Da Kuma Sarkin Katsina
- Tsaro: Gwamnoni Arewa Maso Yamma Za Su Yi Taro Domin Neman Mafita A Katsina
Kazalika maharan sun ƙone motoci guda 9 da gidaje guda huɗu sannan sun ɗauke mutane fiye da hamsin duk a cikin daren.
Majiyar Leadership Hausa ta tabbatar da cewa an ƙone fiye da shaguna 15 ciki harda shagon sayar da magunguna a cikin garin Maidabino a yayin kai wannan hari na ƙare dangi.
Ado Gambo Maidabino na ɗaya daga cikin waɗanda aka konewa shagon sayar da magunguna wato ƙyamis a garin kuma ya bayyana takaicinsa gane da wannan hari.
Yana mai roko Allah ya kawo ƙarshen wannan bala’i tare da fatan Allah ya maida masu da abin da suka rasa.
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗan Musa a majalisar dokokin jihar Katsina Aminu Sai Baba ya tabbatar da faruwar wannan lamari tare da yin Allah dai da kuma kira ga gwamnati ta kawo ɗauki na gaggawa.
Ya kuma ƙara da cewa tuni gwamanti ta amsa kiran su inda yanzu haka an riga an kai jami’an tsaro wannan yanki domin dawowa da zaman lafiya.
Idan za a iya tunawa yankin Ɗan Musa na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga ba dare ba rana.
A gobe litanin ne shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu zai buɗe wani taro akan harkar tsaro da gwamnonin arewa maso yamma da hukumar UNDP suka shirya a Katsina domin shawo kan matsalar tsaro a yankin.