An cafke wata mata mai suna, Aisha Abubakar a jihar Katsina tana dauke da tulin alburusai a tare da ita a cikin wata motar bas mallakin Gwamnatin Jihar Katsina a karshen mako da muka yi bankwana da shi.
An hasko matar a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta na yanar gizo tana ikirarin cewa yunwa ce ta tilasta mata ta karbi aikin safarar alburusan don ta kai wa ‘yan bindiga ba don tana so ba.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 9 Da Sace 50 A Jihar Katsina
- Ƴan Bindiga Sun Ƙone Gidaje Da Motoci, Sun Sace Mutane 50 A Katsina
Matar mai suna Aisha ta amsa tambayoyin jami’an da suka cafke ta cikin harshen Hausa, sai dai Aisha ta musanta cewa tana da hannu a irin wadannan ayyukan na ta’addanci a baya. “Ban taba yin haka ba, yunwa ce ta tilasta ni aikata wannan ma.” Cewar Aisha.
A cewar matar da ake zargi da safarar alburusan, ta ce wani mutum ne ya ba ta amanar alburusan, inda ta ce sam ba ta san ainihin mutumin ko inda yake da zama ba. “Ban san ko menene a ciki ba, wani mutum ne ya ba ni, ban san shi ba kuma ko sunansa ban sani ba ko inda yake zaune.”
Bayan an matsa mata da tambayoyi kan ko ina za ta kai alburusan, Aisha ta ce an umarce ta ne da ta je ta ajiye a rafin Hanyin Dantumaki a cikin Katsina wani zai zo ya dauki jakar daga baya.
Har kawo wannan lokacin da muke hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da kama wannan matar da aka gano da alburusai ba.