Hukumar hana da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kebbi, ta ce akwai alaƙa mai karfi tsakanin miyagun ƙwayoyi da miyagun laifukan, domin amfani da miyagun ƙwayoyi na baiwa masu aikata rashin ganin kowa da gashi da kuma shan ƙwayoyi a cikin al’umma ba tare da jin kunya ba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kwamandan NDLEA reshen Jihar Kebbi, Suleiman Usman, a Birnin Kebbi, a wani jawabi da ya gabatar a taron lacca na ci gaba da bikin tunawa da ranar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara da ake gudanar wa duk ranar 26 da Kuma 27 ga watan Yuni.
Kwamandan ya bayyana cewa magance matsalolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucinsu ya zama wajibi sakamakon munanan dabi’u da aikata ɓarna a cikin al’umma da suke jawo wa.
- Jihar Kebbi Ta Yi Babbar Nasara A Aikin Hajjin Bana – Alhaji Faruk Yaro
- Gwamnatin Gombe Ta Bukaci Jami’an Lafiya Da Su Kara Kwazo Wajen Yaki Da Cutar Sida
A cewarsa, miyagun kwayoyi da aka fi ta’ammali da su a Jihar sun haɗa da Tramadol da Codeine da Benzodiazepines da Exol da methylamphetamine (met, ice) da a Kuskura (Garwan Ganye) da kuma wanda ya fi daukar hankali allurar Pentazocine hade da shisha da tabar wiwi da dai sauransu.
Shugaban taron kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da sufuri Injiniya Umar Faruq Muslim, ya jaddada muhimmanci da kuma wajabcin kawar da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a cikin al’umma, inda Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, kuma jakadiyar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, ta yi alkawarin samar da ƙarin cibiyar farfaɗo da masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi jihar.