Kamfanin CHN Energy na kasar Sin, ya cimma babbar nasara a fannin fadada samar da makamashi mai tsafta, ta hanyar kafa karin na’urorin samar da makamashi.
Kamfanin na CHN Energy ya ce ya zuwa karshen watan Yuni, sassan na’urorin kamfanin na samar da makamashi, sun samar da jimillar lantarki da ya kai kilowatts miliyan 100, lamarin da ya nuna yadda kamfanin ya cimma gagarumar nasara, ta fuskar karkata ga sabbin hanyoyin samar da makamashi mai tsafta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)