• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Halarci Taron Kwamitin Shugabannin Mambobin Kungiyar SCO Ya Kuma Gabatar Da Jawabi

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
SCO

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta tare da gabatar da jawabi a yayin taron kwamitin shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO dake gudana a Astana, fadar mulkin kasar Kazakhstan a safiyar yau Alhamis.

A cikin jawabinsa, Xi ya bayyana cewa, yawan mambobin kungiyar ya karu zuwa 10 bayan shekaru 23 da kafuwarta, inda kungiyar na shafar kasashe 26 daga nahiyoyi 3, wato mambobi 10 da masu sa ido 2 da abokan tattaunawa 14, matakin da ya inganta tushen hadin gwiwarsu sosai.

  • Xi Jinping Ya Gana Da Vladimir Putin
  • Binciken CGTN: 93.1% Na Adawa Da Yunkurin Amurka Na Kafa NATO Irin Na Asiya

Ban da wannan kuma, Xi ya ce, kamata ya yi mu nace ga ra’ayin tsaro na daukar nauyi cikin hadin kai mai dorewa, da tinkarar kalubalolin tsaro masu sarkakiya ta hanyar shawarwari da hadin gwiwa, da kuma magance tsarin kasa da kasa dake fuskantar kyautatuwa bisa ra’ayin hadin kai da cin moriya tare, kana da kafa wata duniya mai dadadden zaman lafiya, da tsaron duniya gama gari, ya kamata a yi hakuri da juna da hanzarta kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha cikin hadin kai, kana da kiyaye gudanar da tsarin samar da kayayyaki yadda ya kamata, har ma da bullo da karfin bunkasa tattalin arzikin shiyyar. Kazalika, da gaggauta samun bunkasuwa tare, da adawa da shisshigi daga ketare da nacewa ga goyawa juna baya, da mai da hankali ga muradun dake jawo hankalinsu, gami da daidaita bambancin ra’ayi cikin lumana, da warware matsalolin dake kawo cikas ga hadin kansu, kana da dogaro da kai wajen samun bunkasuwar kasa da shiyya.

A yayin taron da aka gudanar a yau, mambobin kunigyar sun kulla yarjejeniyar shigo da Belarus a matsayin mambar kunigyar.

Sannan da yammacin Alhamis din nan 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kungiyar “SCO+” a birnin Astana na kasar Kazakhstan, inda kuma ya gabatar da jawabi.

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

Yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai ko (SCO) na wannan karo, kungiyar ta fitar da Sanarwar bayan taro ta majalissar shugabannin kasashe mambobin ta, da manufar SCO ta ganin kasashe mambobi sun dunkule wuri guda, da ingiza zaman lafiya da adalci a duniya, da zaman jituwa da ci gaba, da kuma sanarwar majalissar shugabannin kasashe mambobin kungiyar, game da bin ka’idar makwaftaka ta gari, da amincewa juna da yin kawance.

Kasar Sin za ta rike ragamar shugabancin kungiyar SCO tun daga shekarar nan ta 2024 har zuwa 2025. Kaza lika, za a gudanar da taron faraministocin kasashe mambobin kungiyar a watan Oktoban bana, a birnin Islamabad na kasar Pakistan. (Masu Fassara: Amina Xu, Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 
Daga Birnin Sin

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar
Daga Birnin Sin

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Next Post
An Fitar Da Alkaluman Awon Yadda Ake Hade Ayyukan Masana’antu Da Fasahar AI A Sin

An Fitar Da Alkaluman Awon Yadda Ake Hade Ayyukan Masana’antu Da Fasahar AI A Sin

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.