Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jajanta wa iyalai, gwamnati da al’ummar Jihar Borno bisa munanan hare-haren kunar bakin wake da aka kai a karamar hukumar Gwoza.
Gwamna Inuwa ya yi kakkausar suka ga wannan danyen aiki wadda ya yi sanadin asarar rayukan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba tare da jikkata wasu da dama.
- An Jinjinawa Matakan Kare Hakkin Bil Adama Na Kasar Sin Yayin Zaman Taron MDD
- Muna Jaddada Kiran A Tsame Masarautunmu Daga Rikicin Siyasa
Da yake bayyana harin a matsayin na matsorata, shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa ya jaddada cewa irin wadannan ayyukan ta’addanci abun yin tir ne a cikin al’umma mai zaman lafiya da ci gaba.
“Wadannan hare-haren matsoratan ‘yan ta’adda masu zubar da jini, ba za su taba karya zuciyar al’ummar Arewa masu son zaman lafiya ba,” in ji shi.
Gwamnan ya yaba da irin namijin kokarin da Gwamnatin Tinubu ke yi wajen yaki da ta’addanci duba da matsin lamban da ake yi wa wadannan miyagun mutane.
A sanarwar da kakakinsa, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, Inuwa ya bayyana kwakkwaran imanin cewa idan aka ci gaba da kokari ta hanyar hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, za a dakile wadannan barazanar ta’addanci yadda ya kamata.
“Dole ne mu tabbatar da cewa jami’an tsaronmu a ko da yaushe su na daukan matakan dakile wadannan ‘yan ta’adda. Ingantattun bayanan sirri da daukan matakan da suka dace suna da matukar muhimmanci wajen magance aukuwar irin wannan mummunan lamari,” in ji shi.