Gwamishinan al’amuran addini na Jihar Kano, Hon Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya bayyana cewa cikin muhimman ayyukan da gwamnatin Jihar Kano ta yi karkashin shugabancin Alhaji Abba Kabir Yusuf har da toshe hanyoyin sulalewar kudade daga asusun gwamnatin.
A cewarsa, duk da tulin kalubalen da Gwamnatin Jihar Kano ke fuskanta, hkan bi hana ta aiwatar da samun nasarori kan ilimi lafiya, noma, samar da hanyoyin sufuri, tallafi wa mata da jarin sana’o’i da kuma sauran fannoni na inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.
- Huldar Abotar Dindindin Tsakanin Sin Da Kazakhstan Na Samun Ci Gaba Zuwa Sabon Mataki
- An Sake Wani Mummunan Hatsarin Mota A Kano, Mutane 25 Sun Mutu, 53 Sun Jikkata
Gwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata.
Ya ce dangane da abin da ya shafi addini kuwa, yanzu haka gwamnatin Kano ta gabatar da aikin hajji cikin nasara, musammam wajen talafa wa alhazan jihar da auren zaurawa da kuma yunkurin kammala makarantun a kananan hukomomin Kano.
Gwamishinan ya nemi al’umar su ci gaba da addu’o’i ga gwamnatin Jihar Kano na ganin an samu walwala ta kowacce fuska da kuma samun hadin kasashen Larabawa da ke kokarin tallafa wa Kano ta fuskar ilimin addini da sauran fannoni na ilimi. Sannan ya bukaci mawadata su ba da zakkah ga hukumar kula da fitar da zakkah, domin bai wa takalawa.