Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Kananan Hukumomi Maru Bungudo da ke Jihar Zamfara, Hon Abdulmalik Zubairu Zannan Bungudo, ya aurar da ‘yan mata 105 wadanda suka rasa iyayensu sakamakon matsalar tsaro.
A jawabinsa a wajan daurin auren, Zannan Bungudo, ya bayyana cewa, aurar da ‘yan matan zai taimaka wajan ceto rayuwarsu da kuma samun ingantattar al’umma.
- Dan Majalisa Ya Aurar Da ‘Yan Mata 105 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe Iyayensu A Zamfara
- Sauya Fasalin Dimokuradiyyar Afirka: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Yada Kwallon Mangwaro Mu Huta Da Kuda
“Kuma wadannan matan kowace bayan kayan daki da na yi mata zan ba ta naira 50,000 ta yi jari, su kuma mazajen kowa zan ba shi naira 100,000 su yi jarin kasuwanci don daukar nauyin ‘yan uwansu marayu da aka bar musuu. Kma wannan zai taimaka wajen ingata rayuwarsu ta kowa e bangare,” in ji dan majalisar.
A nasa jawabin babban bako, Satana Kawu Sumaila, ya bayyana cewa, auran wadannan marayu da Hon Abdulmalik Zannan Bungudo ya yi babban jahadi ne don ya ceto wadannan marayu daga halin da suke ciki na kunci da damuwa kuma zai rage masu radadin rashin mahaifansu.
Sumaila, ya kuma jawo ayoyi a cikin Kur’ani wadanda suka wajabta taimakon marayu da kuma alhairin da ke cikin daukar hidamar marayun.
Kuma a nan ta ke Sanata ya ba amaren da mazajansu Naira miliyan biyu da dubu dari q matsayin nasa tallafin a gare su.
Ya kuma yi kira ga ma’auratan da suji tsoron Allah wajen tafiyar da rayuwarsu kuma su sani cewa, aure ibada ne da fatan Allah Ya albarkaci auren ya kuma ba su zuriya dayyiba.