Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya nanata bukatar karfafa jingar dake akwai a fadin kasar, yayin da sassa da dama ke tunkarar ambaliya.
Zhang Guoqing ya yi kiran ne jiya Asabar, yayin gabatar da umarnin takaita ambaliya a hedkwatar hukumar takaita ambaliya da tunkarar fari ta kasar.
- Shugaba Xi Jinping Ya Ba Da Umarni Kan Aikin Tinkarar Ambaliyar Ruwa A Kasar Sin
- Xi Ya Gudanar Da Babbar Tattaunawa Da Shugaban Tajikistan
Ya kuma bukaci hedkwatar ta samar da ma’aikatan agaji da kayayyakin tallafi cikin gaggawa ga lardin Hunan dake tsakiyar kasar, inda aka samu rushewar wata jinga da yammacin ranar Juma’a.
Tun da aka shiga lokacin damina, yankuna da dama na kasar Sin ke fuskantar mamakon ruwan sama. A bana, lardin Hunan ne ya fi fama da mamakon ruwan sama, inda har yawansa a wasu sassa ya kai matsayin koli a tarihi.
Jingar tabkin Dongting ne ya rushe, wanda shi ne tabki na biyu mafi girma a kasar Sin dake zaman ma’adanar ruwa dake kusa da kogin Yangtze.
A cewar mataimakin firaminitan, dole ne hedkwatar ta tallafawa ayyukan ceto a yankuna, domin kare karuwar rushewar Jinga da tabbatar da gyara a kan kari.
Ya kuma bukaci gwamnatocin kananan hukumomi a sauran yankunan da ambaliya ta auku da su sakewa mazauna matsugunai domin kare su daga jikkata. (Fa’iza Mustapha)