Hukumar kula da harkokin yawon buɗe ido ta jihar Filato, ta bayyana cewa an gano Kurar da ta tsere daga gidan ajiyan namun dajin Jos, tare da dawo da ita kejinta.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Babban Manajanta Chuwang Pwajok, ta ce su na godiya ga jama’a bisa haɗin kai, da su ka ba su wanda hakan ya taimaka matuƙa wajen bincike da kamo dabbar.
- CDD Ga INEC: Ku Dabbaka Sahihin Zaben Da Kuka Yi A Osun, Ekiti A 2023
- Bikin Bazara Na Shekarar Dabbar Loong Ya Baiwa Duniya Damar Ganin Muhimmancin Tattalin Arzikin Sin
Idan ba a manta ba hukumar kula da yawon shaƙatawa ta Jihar Filaton, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin kurayen da ke gidan ajiyan namun dajin na Jos ta tsere, inda ya kara da cewa sun tura tawaga ta musamman ta Park Rangers tare da taimakon fasahar jirage marasa matuƙa don nemo ta.
Ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa sun ɗauki duk matakan da suka dace domin gano dabbar da kuma tabbatar da dawowar ta cikin matsugunin ta cikin gaggawa.