Rahotanni sun bayyana cewa an bayar da belin Beatrice, matar Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa.
An bada Belin din ne lokacin da ake shari’a kan zargin da ake yi mata ita da Mijinta na kokarin cire kodar wani yaro dan Nijeriya da suka dauka zuwa Kasar Birtaniya.
Ekweremadu, sanata ne mai wakiltar mazabar Enugu ta yamma.
A cewar wani rahoto da aka fitar a ranar Litinin, an bayar da belin Beatrice ne a lokacin da ta bayyana a gaban kotun manyan laifuka dake Landan, a ranar Juma’a.
Sai dai an ce Kotun taki amincewa ta bayar da belin dan Majalisar (Ike Ekweremadu).