Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bayani kan yadda take kiyaye muhallin halittun teku a yau Alhamis. Takardar mai kunshe da sassa 7, ta kunshi bayanai game da samar da yanayin muhalli mai jituwa tsakanin bil Adam da teku, da gaggauta kiyaye yanayin muhallin teku, da daidaita harkoki a wannan fanni, da ma gudanar da aikin bisa ilmin kimiyya, kana da kara sa ido kan aikin da daga matsayin raya teku ba tare da gurbata muhallinsa ba. Kaza lika da hadin kan sassan kasa da kasa tsakanin mabambantan bangarori na duniya.
Takardar ta kuma nuna cewa, Sin tana kokarin ingizawa, da aiwatar da tsarin kiyaye muhallin halittun teku ba tare da tangarda ba, duba da cewa muhallin halittun teku na da muhimmmanci sosai ga bunkasuwar Sin a fannin kiyaye muhalli.
- Shugaban Kenya Ya Kori Ministocin Kasar Baki Daya Daga Aiki
- Albashi: Shugabannin Kungiyoyin Kwadago Na Gana Wa Da Tinubu A Abuja
A cikin shekaru da dama da suka gabata, Sin ta nace ga mai da muhallin halittu gaba, da gudanar da aikin kiyaye muhalli bisa tsari, da daidaita batun samun bunkasuwa da kiyaye muhalli, ta yadda za a samu bunkasuwa mai inganci bisa tsarin kiyayewa mai karfi, ta yadda hakan zai kafa wani yanayi na jituwa tsakanin bil Adam da teku.
Har ila yau, takardar ta ce Sin na dukufa kan hanzarta hadin kan kasa da kasa wajen kiyaye muhallin halittun teku, da sauke nauyin dake wuyanta na tabbatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa, da ma gabatar da shiri irin na Sin a wannan fanni, wanda hakan ke bayyana cewa, Sin tana cika alkawarinta a wannan fanni. (Amina Xu)