Sarkin Hausawan Afirka kuma Sardaunan Agadas, Dakta Abdulkadir Koguna, ya bayyana cewa sakamakon ci gaba da masarautar Hausawan Afirka take samu yanzu haka, akwai yunkurin samar da katafaran asibiti wanda za a rinka aiki da Hausa zalla, kamar rubutun likitoci da sauran dukkan wasu rubuce-rubuce a Kano.
Dakta Abdulkadir ya bayyana haka ne jim kadan bayan gabatar da nada hakimai biyar da Danmadamin Sarkin Hausawan Afrika, Alhaji Auwalu ya gabata a fadar mai martaba sarkin Hausawan Afirka da aka yi a ranar Asabar da ta gabata a Jihar Kano.
- NLC Da TUC Za Su Sake Sabon Zama Da Tinubu A Mako Mai Zuwa
- Sheikh Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa
Ya ce akwai yunkurin samar da gidan rediyo na Hausa domin bunkasa harshen a wannan Nahiyar Afirka dama duniya baki daya. Ya ce wannan abubuwa na ci gaba sun samu ne sakamakon ci gabar da masarautar Hausawan Afrika take samu a ko da yaushe, wanda da ta zama babbar masarauta mai hakimai 143 a sassa daban-daban a Nijeriya dama Afirka, wanda wannan babban ci gaba ne ga masarautar sarkin Hausawan Afirka.
A karshe, ya bayyana cewa daukakar da Hausa take samu a duniya shi ne dalilin da ya sa ake nuna hassada da kiyayya ta hanyar bata sunan sana’o`in Hausa, kamar da ake ce wa mahauci karan lahira, masinci karni yake. Sarkin Hausawan Afirka ya yi wa Kano, addu’a Allah ya tabbatar da abun da ya fi wa Kanawa zama alkairi kan rikicin masarautar a halin yanzu.