Gwamna Dauda Lawal ya amince da dokar takaita zirga-zirgar babura a Jihar Zamfara daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.
A yau Alhamis ne gwamnan ya rattaba hannu kan dokar a gidan gwamnati da ke Gusau babban birnin jihar.
- Ya Kamata A Lura Da Bukatun Kasashe Masu Tasowa
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli Ta Ba Ƙananan Hukumomi ‘Yancin Cin Gashin Kansu
Babban mataimaki na musamman na gwamna kan yada labarai, Sulaiman Bala Idris ne, ya bayyana haka a takardar da ya sanya wa hannu a Gusau.
A cewarsa kwamitin tsaro ya yanke shawarar takaita zirga-zirgar babura a Zamfara a wani taron gaggawa da ta yi a jiya Laraba.
A cewarsa, an aiwatar da dokar a bisa doka, babban mai shari’a na jihar, Abdul’aziz Sani SAN, ya gabatar da dokar zartarwa mai lamba 07, 2024 ga gwamnan daga bisani ya amince.
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a fadin Jihar Zamfara.
“Wannan wani kokari ne na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da dakile kalubalen tsaro da fadada hanyoyin da gwamnati za ta dauka na karfafa yaki da ‘yan fashi da sauran munanan dabi’u a jihar.
“A yanzu haka duk babura an hana su yawo a jihar daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.
“Babu babur da aka bari ya yi tafiya a kowace hanya a jihar cikin wadannan sa’o’i. An umurci hukumomin tsaro da su kama duk wanda ya karya wannan umarni.
“Atoni Janar na Jihar Zamfara yana da ikon gurfanar da wadanda suka ki bin dokar gaban kotu.”