Duk da sa bakin wasu da ake kallo a matsayin wadanda karansu ya kai tsaiko, ku-ma ake da kyakkyawan zaton idan suka ce ga yadda za a yi, to za a yi wa tufkar hanci, amma dai har yanzu kura tukunyar rikicin masarautun Kano na ci gaba da kara tafasa.
Wannan shi ne irinsa na farko a tarihin masarautar Kano, masu sarhi sun hakikance cewar siyasa ce ke zaman musabbabin wannan danbarwa. Wanda kuma idan ba a yi wa tufkar hanci ba, za ta iya zama wata gobara daga teku. Mu-samman Ganin yadda lamarin ya fara yaduwa zuwa wasu masarautun wadan-da zuwa yanzu aka jin yadda aka fara yamutsa gashin baki.
- Ganduje Da Mai Dakinsa Za Su Gurfana A Gaban Kotu A Kano
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-zirgar Ababen Hawa
Yanzu haka an fara jin motsin irin wannan matsalar ta fara fitowa a wasu jihohi biyu na arewacin kasar nan, wanda suka hada da Sakwato da Katsina. A Jihar Sakwato har an kai irin wannan kudiri gaban majalisar dokokin jihar, inda ake za-ton irin wannan guguwar na neman yin awon gaba da rawanin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar. Yayin da a Jihar Katsina kuwa, shi ma Mai Martaba Sarkin Kataina, ya karbi takardar da ke neman ya yi bayanin dalilinsa na kin yin hawan sallar da ta gabata.
Yanzu haka lamarin kullum daukar sabon salo yake a Masarautar ta Kano, domin kamar yadda aka sani sarakuna biyu ke mulki a Kano, guda ya samu rakiya tare da kariyar gwamna, wanda aka shigar da shi gidan Rumfa cikin dare, yayin da daya bangaren kuma yake gudanar da mulki daga gidan Nassarawa, wurin da ke samun tsaro daga jami’an ‘yansanda da sojoji.
A bangaren rundunar ‘yansanda kuwa, ta shelanata yin tsayuwar daka kancewar tana bin umarnin kotu ne, don haka take bayar da kariya ga Sarki Aminu Ado Bayero, inda wata kotu ta dakatar da Gwamnan Abba Kabir Yusuf daga ci gaba da daukar kowane irin mataki a kansa har sai ta kammala shari’ar da ke gabanta.
Sai dai kuma gwamna ya sa kafa ya yi fatali da umarnin na kotun, ya rattaba wa dokar hannu da aka yi wa kwaskwarima tare da damka wa Muhammadu Sanusi II takarda sake dawo da shi a matsayin sarkin Kano na 16.
Haka zalika, ana ta samun mabanbantan tunani, inda wasu ke tururuwar zuwa fadar gidan Runfa domin yin mubayi’a ga Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II, mu-samman jami’an gwamnati da masu biyayya ga darikar kwankwasiyya, wannan tasa wata kididdiga ta nuna cewa Sarkin Kano na 16 ya karbi mubayi’ar hakimai sama da guda 40, wanda kuma wannan kamar yadda wata majiya ta tsegunta wa wakilinmu na samun umarnin zuwa mubayi’ar ne daga fadar gwamnati, kuma suna zuwa domin gudun asarar rawaninsu.
Kamar yadda aka sani akwai kararraki har guda uku da ke gaban kotuna, inda wa-ta kotun tuni ta yi fatali da nade-naden da gwamna ya yi ta kuma tabbatar da ce-wa, Aminu Ado ne halastaccen Sarki. Bayan yanke wannan hukunci ne kotun ta mika wa kotun da bangaren gwamnati ta daukaka kara domin ci gaba da shari’ar. Haka kuma akwai kotun da tuni ta yanke hukunci tare da cin tarar gwamnatin Ka-no har naira miliyon 10.
Sannan akwai kotun da gwamnatin Kano tare da majalisar dokokin Jihar Kano su-ka kai kara, inda kotun ta ba da umarnin lallai a fitar Sarki Aminu Ado Bayero daga gidan Nassarawa. Wannan kotun na karkashin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu.
A cikin makon da ya gabata ne kuma aka wayi gari da ganin an tayar da tuta a gidan Sarki Nassarawa, wanda hakan wata shaida ce da ke nuna cewa sarki na nan, kuma bisa muhimmancin wannan tuta wadda ita ce shaidar tutar da Shehu Usman Danfodio ya raba wa sarakunan Musulunci.
A martanin daya bangaren ta bakin shugaban jam’iyyar NNPP, Alhaji Hashimu Dugurawa ya bayyana cewa wannan tuta ba ta wuce kokarin da wani ke yi na ku-la da makabartar da ake bizne iyayensu a ciki ba.
Dugurawa ya ce wadancan sarakuna biyar ba su da maraba da kwamishinoni, domin an nada su ne saboda su taimaka wa Ganduje cin zabe, kuma ya fadi, don haka a cewarsa ya yi mamakin da tuni ma ba su sauka daga kujerun da suke kai ba kasancewar shi ma Ganduje ya bar tasa kujerar.
Yanzu haka dai an samu matsayar kutna biyu cikin ukun da ke gaban alkalai, inda kutuna biyu suka zantar da hukuncin da ke nuni ga halascin Sarkin Aminu Ado Bayero, duk da cewa kotun gwmanatin ta yanke hukunci ne kan nade-naden da Ganaduje ya aiwatar bayan samun umarnin kotu na tsaya wuri guda har zuwa lo-kacin da kotun za ta kammala sauraron korafin da aka gabatar mata.
Gwamna Abba ya yi tali da umarnin na kotu duk irin kallon da duniya ke masa na cewa shi kansa ribar hukuncin kotuna yake ci, domin da kotu ba ta ba shi nasara a shari’ar da kowa ya yanke tsammanin samun nasarar jam’iyyar NNPP ba, sakamakon hukuncin kwace kujerar har karo biyu da kotun farko da ta biyu suka yi.