Babban Hafsan Sojin Kasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ce matukar al’ummar karkara ba su samu ci gaba ba, zai yi wuya a kawo karshen rashin tsaro a Nijeriya.
Dangane da haka, Babban Hafsan ya ce bai wa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kai, ko shakka babu zai magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.
- Cika Shekara 100 A Duniya: Tarihin Shaikh Dahiru Bauchi Daga Bakinsa
- Za A Samar Da Asibitin Da Zai Yi Amfani Da Hausa Zalla -Sarkin Hausawan Afrika
Janar Lagbaja ya bayyana haka ne a yayin bikin da sojojin Nijeriya aka gudanar a Jos, Babban Birnin Jihar Filato a ranar Juma’a. Ya kuma jaddada cewa matukar al’ummomin karkara ba su samu ci gaba ba, zai yi wuya a kawo karshen rashin tsaro a kasar.
“Me ya sa jiga-jigan ‘yan siyasa ke bijire wa ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi, wanda jama’a ke kokawa a kai, hanyar da ta fi dacewa wajen kawo ci gaba a matakin kasa shi ne tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi, ba wai ta hanyar kafa kwamitoci ko na ofis ba, mun riga mun kafa ma’aikatu, har sai mun yi aiki, dole a dauki ci gaba zuwa matakin kasa.
“Ga wadanda suka san yanayin Arewa-maso-Gabas, lokacin da aka tura ni Bataliya ta 93 a shekarar 1992, a wancan lokacin abu ne mai sauki a cikin sa’o’i uku ka yi tafiya daga Maiduguri zuwa Munguno, Kukawa da sauran wurare, amma a yau abin ba zai yiwu ba, kyakkyawan shugabanci a matakin kananan hukumomi babu shi a yanzu, kuma wannan shi ne ke kawo rashin tsaro a kasar nan ba wai a yankin Arewa maso Gabas kadai ba, har ma a yankin Arewa ta Tsakiya da sauran yankuna.” Inji Janar Lagbaja.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a baya gwamnonin jihohi sun ki amincewa da yunkurin bai wa kananan hukumomin kasar cin gashin kai. Sai dai gwamnatin tarayya na yin wani yunkuri na bai wa kananan hukumomin cin gashin kansu.