Sanarwar ta Jamus dai na zuwa ne a wani lokaci da kasar ta Nijar ta kawo karshen yar-jejeniya da wasu kasashen Yammacin duniya irin su Amurka da Faransa.
A cikin wata sanarwa ce da ma’aikatar harakokin wajen Kasar Jamus ta fitar inda ta ce kasar za ta rufe sansanin sojojinta dake Nijar a ranar 31 ga watan Au-gusta mai kamawa bayan da kasashen biyu suka kasa cimma matsaya kan tsar-in bayar da horo da kuma makamai.
- Kasar Sin Ta Yi Kakkausar Suka Kan Kalaman Tsokana Da Sakatare Janar Na Kungiyar Tsaro Ta NATO Ya Yi Kan Kasar
- Cika Shekara 100 A Duniya: Tarihin Shaikh Dahiru Bauchi Daga Bakinsa
Sansanin na zaman wata hanyar yakar ta’addanci ne a kasashen yankin Sahel karkashin kulawar Majalisar Dinkin duniya.
Sai dai masana harkokin yau da kullum irin su Abdurahmane Dikko na ganin ficewar dakarun kasar Jamus daga Nijar ba zai rasa nasaba da sabuwar alakar dake tsakanin Nijar da kuma Rasha ba.
Wannan matakin na Jamus ya kara jaddada irin tsamin dangantaka dake tsa-kanin kasashen Yamma da kuma hukumomin mulkin sojin Nijar, to sai dai Al-kassoum Mato masanin harkokin tsaro a Nijar ya bayyana dalillan da suka sanya Jamus daukar wannan matakin na ficewa daga kasar Nijar akan batun shigar Rasha kasar ne.
A lokutan baya dai Jamus ta bukaci kulla yarjejeniya ta wucin gadi da kasar ta Nijar ne, sai dai ga dukkan alamu ficewar dakarun kasashen Faransa da Amurka daga Nijar ya kawo cikas ga kasasncewar Jamus a wannan kasa ta yankin Sahel.