Gwamnatin Nijeriya da ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) sun yi nasarar cimma yarjejeniyar barin masu riƙe da fasfo na Nijeriya su koma yin tafiye-tafiye zuwa ƙasar ta UAE.
Wannan cigaban ya biyo bayan tattaunawa mai yawa kuma mai amfani tsakanin ƙasashen biyu.
- Fityanul Islam Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Da Ake Shirin Yi
- Messi Ya Kafa Sabon Tarihi A Ƙwallon Ƙafa Bayan Lashe Kofin Copa America
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya ba da sanarwar yarjejeniyar.
Za a fara maido da bai wa ‘yan Nijeriya bizar zuwa UAE daga ranar 15 ga Yuli, 2024, tare da sababbin sharuɗɗan samun bizar.
‘Yan Nijeriya da ke son duk wani ƙarin bayani game da sharuɗɗan bizar da UAE ta sabunta za su iya ziyartar gidan yana kamar haka:
documentverificationhub.ae