Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu ta jihar Kano ta shekarar 2024, wacce ta kafa sabbin masarautu guda uku a jihar.
Gwamnan, yayin da yake godewa majalisar dokokin jihar kan yadda ta saurari bukatun jama’a, ya kuma yaba da yadda ‘yan majalisar dokokin jihar suka jajirce wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu.
- Masana’antar Kera Jiragen Ruwa Ta Sin Na Ci Gaba Da Samun Tagomashi A Farkon Rabin Shekarar Bana
- Gdpn Sin Ya Karu Da Kashi 5% A Watanni Shida Na Farkon Bana
Sabbin masarautun guda uku sun hada da masarautar Gaya da ta kunshi kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu; Masarautar Rano ta kunshi kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, sai kuma masarautar Karaye, wadda ta kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo na jihar.
Shugaban Majalisar, Jibril Falgore ne ya mika wa Gwamnan Jihar kudirin dokar a fadar gwamnati da ke gidan Gwamnatin Jihar.
Shugaban majalisar ya godewa gwamnan jihar bisa bai wa majalisar jihar hadin kai tare da yin alkawarin ci gaba da yin hadin gwiwa.