Ministar Matasa, Dr. Jamila Ibrahim, ta ce akalla matasa miliyan daya ne za su ci gajiyar shirin horar da matasa na kasa, NYSP, a shekarar farko ta kaddamar da shirin.
Dr. Jamila ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a wajen taron tunawa da ranar basirar matasa ta duniya na shekarar 2024 mai taken, “koyar da sana’a ga matasa don zaman lafiya da ci gaban su”
- Yanzu-yanzu: Gwamna Yusuf Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Samar Da Masarautu Uku Masu Daraja Ta Biyu A Kano
- Matsalar Karancin Abinci Za Ta Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamnatin Tarayya
A cewar ministar, bikin ya yi daidai da bukatar Majalisar Dinkin Duniya na ware ranar 15 ga watan Yulin kowacce shekara don gudanar da bikin wannan rana.
Misis Ibrahim ta ce, taron na shekara-shekara ya kasance wata dama ce ga kasashe mambobin kungiyar su gane mahimmancin baiwa matasa sana’o’in yi da kasuwanci.
Ta ce taron na da nufin magance kalubalen koyon sana’o’i a tsakanin matasa.
Ta ce nan, ba da dadewa ba za a kaddamar da shirin NYSP, inda Matasa miliyan daya za su amfana da shirin a shekarar farko.