Bayan kwashe watanni ana kai ruwa rana, gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun amince da biyan Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis bayan ganawar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi da shugabannin kungiyar kwadago a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Malamin Tsangaya Ya Shiga Hannu Kan Zargin Luwadi Da Ɗalibai A Jigawa
- Kamfanin Sin Ya Fitar Da Sabon Nau’in Karafan Kafafun Jiragen Kasa Masu Saurin Tafiya
Har ila yau, da yake karin haske kan bayanan Ministan, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce, shugaba Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan Nijeriya tare da alkawarin sake duba dokar mafi karancin albashi na kasa duk bayan shekaru uku.
Onanuga ya ce, Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa kamfanoni masu zaman kansu ta yadda za su biya sabon mafi karancin albashin.