Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da Umarnin gudanar da cikakken bincike kan Bidiyon dukan Abdulmajid dan Bilki Kwamanda, wanda yake yawo a kafafen sada zumunta.
A wata sanawar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnatin jihar Kaduna, Muhammad Lawal Shehu, yace gwamnatin ta nisanta kanta akan lamarin.
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Amince A Kan N70,000 Mafi Ƙarancin Albashi
- Malamin Tsangaya Ya Shiga Hannu Kan Zargin Luwadi Da Ɗalibai A Jigawa
“An ja hankalin gwamnatin jihar Kaduna game da wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda aka nuna wasu da ba’ a san ko su wanene ba su na yi wa dan Bilki Kwamanda bulala bisa zargin shi da zagin gwamna Uba Sani”
Sanarwar ta ci gaba da cewa “Gwamnatin jihar Kaduna dai ta nisanta kan ta daga mummunan lamarin, ta na mai cewa, hakan ba ya da hurumi a duk wata al’umma tagari, don haka ta na nan a kan bakan ta na mutunta tsarin bin doka da oda.”
Haka kuma, gwamnatin jihar Kaduna ta ce, tsarin shugabancinta an gina shi ne a kan adalici da daidaito da kuma mutunta dan Adam.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta na maraba da shawarwarin al’umma, sannan ta bude kofar da kowa zai iya bayyana ra’ayinsa a siyasance.
Ta ce Gwamnan jihar Kaduna ya kwashe tsawon lokaci ya na fafutukar kare ‘yancin dan Adam, don haka, har yanzu ya na kan bakan shi na tabbatar da ganin ba a tauye hakkin kowane bil-Adama ba bisa tsarin doka da oda.
Tuni dai Gwamna Uba Sani ya bada umurnin a gudanar da kwakkwaran bincike a kan mumman lamarin, sannan ya lashi takobin bin diddigin yadda lamarin ya faru, tare da bada tabbacin cewa duk mai hannu a aika-aikar dole ya fuskanci hukuncin abin da ya aikata.