Alamu dai na nuni da cewa fafutukar neman jan akalar jam’iyyar PDP gabanin zaben 2027, ya rikiɗe ya koma zuwa jihohi, a daidai lokacin da jam’iyyar ke shirin gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar a jihohi 20.
Rahotonni sun bayyana cewa za a gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar ne a jihohi da suka hada da Akwa Ibom, Bayelsa, Kurus Ribas, Delta, Ribas, Kano, Katsina, Benuwai, Kaduna da Filato, a ranar 31 ga watan Agusta.
- Ranar Dimokuraɗiyyar: Ƴan Nijeriya Fushi Suke, PDP Ga Tinubu
- Rikicin PDP: Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Caccaki Wike
Sauran jihohin da ake sa ran gudanar da zaben shugabannin sun hada da Taraba, Bauchi, Gombe, Inugu, Imo, Abiya, Ogun, Ondo, Ekiti, Edo, Anambra da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wata takarda da aka samu a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa a karshen mako, ta nuna cewa za a yi taron gundumomi da na kananan hukumomi a jihohin da abin ya shafa a ranakun 27 ga watan Yuli da 10 ga watan Agusta. A ranar 26 ga watan Satumba ne ake sa ran kwamitin zartarwa na PDP zai yi taro domin amincewa da dukkan zababbun shugabannin zartaswa da kuma cimma matsaya kan batun babban taron jam’iyyar na kasa wanda zai bayar da damar a zabi shugaban jam’iyyar na kasa.
Majiyarmu ta bayyana cewa a daidai lokacin da za a gudanar da zabukan sabbin shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, manyan ‘yan jam’iyyar adawa sun karkata akalarsu zuwa jihohin.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP na fama da rikice-rikice a jihohi 12 da suka hada da Kano, Katsina, Ribas, Edo, Ebonyi, Ogun, Filato, Neja da Kuros Ribas, da kuma yankin kudu maso gabas. Shugabannin jam’iyyar PDP a jihohin da abin ya shafa sun shiga fafatawa don ganin sun mallaki akalar jam’iyyar gabanin zaben 2027.
Tun bayan zaben 2023, magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun shiga takun saka a kan jan akalar jam’iyyar PDP gabanin zaben 2027.
Kafin taron karshe na kwamitin zartarwa na kasa da jam’iyyar ta gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu, bangarorin biyu sun fafata kan ko wane ne daga cikinsu zai samar da sahihin shugaban jam’iyyar na kasa. Sai dai kwamitin zartaswa na jam’iyyar ya dage zaben sabon shugaban jam’iyyar na kasa har zuwa taronta na gaba wanda aka shirya za a yi a ranar 26 ga Satumban 2024.
A kwanakin baya ne dai wasu daga cikin kwamitocin rikon kwarya sun umurci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar a jihohinsu da su sake tantance mambobinsu a gaban taron, a matsayin wani bangare na kara karfi gabanin zaben jam’iyyar a matakin jiha. Sai dai a wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba ya fitar, ya ce kwamitin gudanarwa na jam’iiyar ya yi watsi da kwamitocin, inda ya ce babu wani tsohon mamba da ake sa ran za a sake tantance shi.
Wata majiya mai karfi a sakatariyar PDP ta shaida cewa, sake tabbatar da mambobin jam’iyyar wata dabara ce da wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar suka yi don ganin sun fatattaki abokan hamayyarsu a fafatawar da suke yi na jan akalar jam’iyyar. “Kuna sane cewa kwanan nan kwamitin gudanarwa na kasa ya ce tsofaffin membobin ba dole ba ne a sake tantancesu. Wadanda za su kada kuri’a ‘yan jam’iyya ne masu rajista. Abin da wadancan mutanen suke yi, suna cewa kowa ya je ya gyara. Don haka, za su dauki katunan da fom, ba za su ba wa wasu mutane ba. Yana daga cikin fafutuka na kula da tsarin jam’iyya.
“Jam’iyyar ta fitar da sanarwar cewa sabunta rajista ba na tsofaffin mambobin ba ne. Yanzu duk ‘yan jam’iyyar ne za su kada kuri’a. Abin da suke so su yi shi ne a hana wasu mutane rike katunan jam’iyyar. A cikin wadancan jihohin da ake fama da rikici, wasu bangarori sun yi kokarin kawar da abokan hamayyarsu. Amma nan da nan aka fitar da wannan sanarwa, an shawo kan lamarin baki daya.”
Wani shugaban jam’iyyar daga kudu maso gabas shi ma ya shaida cewa, “Ka san muna da bangarori da suka hada da na Atiku da na Wike. Har yanzu akwai wani bangare na uku wanda ya kunshi mutanen da ba su yarda da Wike da Atiku ba. Wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP na yin gangami ne domin mayar da jam’iyyar kan hayyacinta. Kamar yadda kuka sani, wadanda aka zaba ne za su yanke shawarar yadda jam’iyyar za ta kasance a gaba. Wadada aka zabe ne za su nuna wadanda ke rike da mukamai.”
A daidai lokacin da ake tunkarar zaben shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, tashin hankali na ci gaba da faruwa a jihohi 12, yayin da jiga-jigan jam’iyyar ke fafutukar ganin sun mallaki akalar jam’iyyar.
Alal misali, shugabannin jam’iyyar adawa a Ebonyi sun ja kunnen ‘ya’yan jam’iyyar PDP wajen kokarin neman shugabanci.
“Ana wannan fafutuka ne domin tsayawa takara a zaben 2027 a jihar. Wasu jiga-jigan da ba su da nasaba da jama’a suna dagewa ne domin su mallaki jam’iyyar gabanin zaben gwamna mai zuwa,” wani dan jam’iyyar a jihar ya shaida haka.
Har ila yau, a Jihar Edo, mambobin kungiyar ‘Legacy Group’ karkashin jagorancin Cif Dan Orbih sun yi artabu da Gwamna Godwin Obaseki kan yadda ake jan akalar jam’iyyar. Wani jigo a jam’iyyar ya shaida cewa ‘ya’yan kungiyar ba su taka kara sun karya ba sakamakon dakatar da Orbih a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa da kwamitin gudanarwa ya yi.