Gwamnatin tarayya ta ce, ta kammala dukkanin shirye-shiryen da suka dace na raba tirelolin shinkafa guda 20 ga kowace jiha daga cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, domin ganin an rabar wa talakawa da suke fama da talauci da fatara a wani yunkuri na kawo karshen matsalar yunwa da ake ciki a fadin kasar nan. Â
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, shi ne ya shaida hakan a ranar Litinin biyo bayan zaman majalisar zartaswa ta kasa wanda Shugaban kasa, Bola Tinubu ya jagoranta.
- Sin Ta Kaddamar Da Mataki Na Biyu Na Tallafawa Madagascar Shuka Shinkafa Mai Aure
- Ina Iya Kera Na’urorin Da Suka Fi Na Kasashen Waje Inganci, In ji Adam
A cewar ministan, majalisar zartaswar ta tattauna sosai kan yadda za a shawo kan matsalolin karancin abinci a fadin kasar nan, don haka ta umarci a rabar da tireloli 20 na shinkafa ga kowace jiha domin rabarwa ga marasa karfi a cikin al’umma don yaki da yunwa.
Ya ce, “Majalisar zartaswar Nijeriya ta yi muhawara sosai kan yadda za a samu raba abinci da kuma kawo karshen karancin abinci a kasar, don haka, zuwa yanzu tireloli 20 na shinkafa tuni aka rabar da su ga kowace jiha ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
“Gwamnatin tarayya ta amince da hakan a matsayin matakin farko na rage kaifin matsin rayuwa da jama’an Nijeriya ke ciki, amma abincin zai je hannun marasa karfi ne kawai da suke cikin al’umma,” ya tabbatar.
Sai dai masu sharhi na yau da kullum suna ganin cewa shin kafan ba za su isa zuwa talakawan da ake bukata, domin a baya ai gwamnati ta yi irin wannan kokari amma kuma abun bai yi nasara ba.
Haka kuma wasu na ganin cewa tirilolin shinkafa guda 20 ba abin da zai iya yi a jihohin, domin mabukata suna da matukar yawa a Nijeriya.