Wani abu da ba a tada a yi ba a tarihin gasar cin kofin Nahiyar Turai da aka kammala a kasar Jamus da kasar Spaniya ta lashe shi ne, hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai da take shirya gasar ta ba wa ‘yan wasa shida kyautar takalmin zinare kasancewar kowanne daga cikinsu yana da kwallaye uku.
Kyaftin din tawagar Ingila, Harry Kane ya karda i kyautar takalmin zinare a Euro 2024 tare da ‘yan wasa biyar a matakin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye kamar yadda hukumar ta yi alkawari.
- Newcastle Ta Kori Manchester City A Gasar League Cup Ta Kasar Ingila
- Spain Ta Lallasa Ingila A Wasan Ƙarshe Na Kofin Euro 2024
Sauran da suka karda i kyautar sun hada da dan wasan Sifaniya, Dani Olmo da na Georgia, Georges Mikautadze da na Netherlands, Cody Gakpo da na Sloda akia, Ida an Schranz da kuma na Jamus, Jamal Musiala. Kane da Olmo sun buga wasan karshe ranar Lahadi a birnin Berlin, amma ba wanda ya zura kwallo a karawar da Sifaniya ta doke Ingila 2-1 wanda hakan ne ya sa dole aka hakura aka ba wa mutum shida.
A baya a kan tantance gwarzo, idan aka duba yawan kwallon da ya ci da wadanda ya bayar aka zura a raga, amma a Euro 2024 UEFA ta ce da yawan cin kwallaye za ta yi amfani. Kane, mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, mai shekara 30 ya ci Denmark da Sloda akia da kuma Netherlands a Euro 2024, kuma shi ne ya lashe kyautar takalmin zinare a gasar Bundesliga ta Jamus da ta wuce, wanda ya zura kwallo 36.
Tsohon dan wasan Tottenham shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar Ingila kwallaye a tarihi, kuma shi ne ya lashe kyautar a kofin duniya a shekarar 2018, wanda ya zura shida a raga.
Dan wasan Sifaniya da Manchester City, Rodri, shi ne ya lashe kyautar fitatcen dan kwallo a Euro 2024 haka kuma Lamine Yamal na Sifaniya da Barcelona shi ne matashin dan wasan gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.