An gudanar da cikakken zama na 3 na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Sin karo na 20, tun daga ranar 15 zuwa 18 ga wannan wata a nan birnin Beijing, inda aka zartas da kudurin kwamitin tsakiya na JKS, game da yadda za a zurfafa yin kwaskwarima, da sa kaimi ga zamanintarwa irin ta kasar Sin, wanda ke kunshe da shirye-shiryen da za a aiwatar a wannan fanni ta hanyar kimiyya, da tabbatar da abubuwan da za a yi gyare-gyare a kai, da kuma yadda za a yi kwaskwarima.
Hakan na nuna yadda za a sa kaimi ga zamanintarwa irin ta kasar Sin yayin da aka kama sabon tafarki, kana ya shaidawa duniya imanin Sin kan yin kwaskwarima da samun moriya tare.
- MDD Ta Nemi A Gaggauta Cimma Muradun Ci Gaba Mai Dorewa Don Cimma Burin 2030
- Bude Kofofin Kasar Sin Muhimmin Mataki Ne Na Ingiza Ci Gaba Da Wadatar Duniya
Wani sharhi game da hakan, ya nuna cewa taron ya zama muhimmin mataki na kasar Sin a fannin zurfafa yin kwaskwarima.
Bude kofa ga kasashen waje, alama ce ta zamanintarwa irin ta kasar Sin. Sin ta samu nasara kan manufofin sa kaimi ga yin kwaskwarima, da samun ci gaba ta hanyar bude kofa ga kasashen waje, kana ta samar wa duniya fasahohinta na raya tattalin arzikin duniya ta bude kofa.
A gun cikakken zaman na wannan karo, an gabatar da sabbin shirye-shiryen sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje zuwa sabon matsayi, wadanda suke shafar manufofin bude kofa bisa tsari, da yin kwaskwarima kan tsarin cinikin waje, da harkokin zuba jari daga ‘yan kasuwan ketare, da kuma zuba jari ga kasashen waje, da kyautata tsarin bude kofa a yankuna, da sa kaimi ga raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya mai inganci da dai sauransu.
Sassan kasa da kasa za su kara sanin cewa, Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, da kuma maraba da bangarorin kasa da kasa da su yi hadin gwiwa tare da Sin, a sakamakon samun bunkasuwar kasar Sin.
Kowace kasa na iya samun zamanintarwa ba lallai ta tsarin kasashen yammacin duniya kadai ba, wato dai sassan kasa da kasa na iya zabar hanyar da ta dace da yanayinsu.
Kasar Sin ta sa kaimi ga zamanintarwa irin ta kasar Sin, kuma hakan ta shaida sabon zabin kasashe masu tasowa wajen samun zamanintarwa, kana ta samar da fasahohinta bisa tsarin gurguzu ga dukkanin bil Adama. (Zainab Zhang)