Wani Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Afam Osigwe, ya zama zababben shugaban kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA).
Sakamakon zaben 2024 na NBA da aka gudanar a yanar gizo kuma wakilinmu Osigwe ya lura da yadda zaben ke gudana, ya bayyana cewa, tsohon babban sakataren NBA, Osigwe ya samu kuri’u mafi yawa a zaben.
- Kotu Ta Wanke Tsohon Dogarin Bukola Saraki Kan Zargin Biliyan ₦3.5b
- Dalilin Raguwar Rikicin Manoma Da Makiyaya A Jihar Gombe
Haka kuma, Misis Bridget Ijeoma Edokwe ta zama Sakatariyar Yada Labarai ta kungiyar.
An fara kada kuri’a ne da karfe 12 na dare a ranar Asabar wanda aka kuma kammala da karfe 1.59 na rana, an gudanar da kada kuri’u da nuna sakamakon ne kai tsaye a shafin https://go.ecnba.org/results/
Osigwe ya samu kuri’u 20,395, inda ya kayar da abokin hamayyarsa kuma shugaban hukumar kula da harkokin shari’a ta NBA, Tobenna Erojikwe, wanda ya samu kuri’u 10,970 yayin da tsohon shugaban NBA reshen Legas, Chukwuka Ikwuazom (SAN), ya samu kuri’u 9,007.
Osigwe na shirin maye gurbin shugaban NBA mai barin gado, Yakubu Maikyau (SAN).