Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), ta koka da yadda rashin tsaro, talauci da jahilci ke jefa yankin Arewa a baya.
A jawabinsa na ranar Litinin a Kaduna, yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Uba Sani a gidan Sir Kashim Ibrahim, shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Usman ya bukaci shugabanni da al’ummar yankin da su gaggauta sauya tunani da tsare-tsare marasa kyau ba tare da bata lokaci ba.
- Zanga-zanga: Minista Ya Nemi Jama’a Su Ƙara Haƙuri, Gwamnati Na Ƙoƙarin Rage Tsadar Rayuwa
- Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Don Tantancewa
Shugaban ACF ya ce: “A cikin kokarinmu, da shugabannin Arewa, da suka hada da gwamnonin jihohi, sarakuna, da sauran dattawa, sun yanke shawarar kafa ACF a shekarar 2000. Saboda bada shawarwari ta yadda za a kawar da irin wannan matsalar ta tsaro da rigingimu a yankin.
“Manufar ita ce, a hada kai a zama daya wajen wakiltar al’ummomin Arewacin Nijeriya ba tare da la’akari da siyasa, kabilanci, ko addini ba. ACF ita ce ta yi aiki a matsayin Majalisar Jama’a ko Dattawa wacce ta buɗe idanu da kunnuwa don yin la’akari da al’amura da ci gaban da ka iya haifar da rashin jituwa, ko rikici a fadin Arewa da bunkasa ci gaban yankin
“A yau, duk da jajircewar da muka yi, samun zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a Arewa, lamari ne da dole sai an jajirce wajen kokarin gudanar shi. Duk alkaluman da ke nuna koma baya a ci gaban bil’adama – talauci, jahilci, da rashin tsaro na rayuka da dukiyoyi – sun jefa Arewa a cikin rami mai zurfi, lallai akwai babban aiki da ke jiran duk ’yan Arewa.”
A cewarsa, ACF ta himmatu wajen bayyanawa da kare muradun al’ummar Arewa ta hanyar ayyukansu daban-daban.
“Daya daga cikin irin ayyukan kungiyar shi ne, kwamitin fasaha da aka kafa kwanan nan wanda ya sake nazarin kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Rahoton kwamitin ya hada alakar ACF da kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa kan sake duba kundin tsarin mulki. Ba da jimawa ba, za a gabatar da rahoton kwamitin fasaha na ACF ga kungiyar gwamnonin Arewa,” Inji Usman