An sako wani dan TikTok da ke Kano, Junaidu Abdullahi, wanda aka fi sani da Abusalma, wanda aka kama tare da tsare shi a gidan gyara hali da ke Kurmawa a Kano saboda faifan bidiyonsa na kiran zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da za a yi a fadin kasar nan a ranar 1 ga Agusta.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama Abusalma a Kano a makon jiya bayan kiran da ya yi na zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a kasar da kuma kin amincewa da kiran wani Malami na janye kiran zanga-zangar a Arewacin Nijeriya.
Sai dai wani mawallafin jarida ta yanar gizo kuma mai fafutukar ‘RevolutionNow’, Omoyele Sowore, a yammacin ranar Talata, ya ce, “daga karshe an sako Abusalma daga tsare shi, biyo bayan ziyarar da lauya mai kare hakkin #EndBadGovernance ya kai a gidan gyaran hali na Kurmawa.”