Yau Laraba, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya tattauna da ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.
Wang Yi ya ce, kasashen Sin da Ukraine abokai ne na juna, kuma abin dake tattare da mu’amalar dake tsakanin bangarorin biyu shi ne sada zumunci da hadin gwiwa. Rikicin Ukraine ya shiga shekara ta uku, kuma a ko da yaushe kasar Sin ta jajirce wajen inganta warware rikicin ta hanyar siyasa. Kwanan baya, kasashen Ukraine da Rasha sun aike da sakonnin da zummar yin tattaunawa, bangren Sin na goyon bayan duk wani kokari da zai samar da zaman lafiya, kuma yana son ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tsagaita bude wuta da daina yaki da kuma sake dawo da tattaunawar zaman lafiya.
Kuleba ya ce, kasar Sin kasa ce mai girma. Ukraine na mai da hankali sosai kan ra’ayoyin kasar Sin, kuma ta yi nazari sosai a kan “Ra’ayoyi shida” da kasashen Sin da Brazil suka cimma kan batun warware rikicin Ukraine a siyasance. Ukraine tana so kuma tana shirya shiga tattaunawa da Rasha.(Safiyah Ma)