Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta dakatar da Akomolafe Gbenga Michael, daya daga cikin ma’aikatanta a filin jirgin saman Murtala Muhammad (MMIA) saboda zargin safarar miyagun kwayoyi.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, kakakin hukumar NIS, DCI Kenneth Udo, ya tabbatar da dakatarwar tare da bayyana cewa, a halin yanzu, jami’in na fuskantar shari’a a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Legas.
- Sakataren Gwamnati Da Ministoci Na Ganawar Sirri Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
- Za Mu Bai Wa Masu Zanga-zanga Kariya Idan Ta Lumana Ce – Sufeton ‘Yansanda
Ya kara da cewa, NIS na ba da cikakken goyon bayan shari’ar da nufin tantance matakin laifin Michael.
NIS ta kuma sake jaddada aniyar ta na kiyaye ka’idojin aiki don kiyaye mutuncin kasa, kuma ba za ta lamunci wasa, sakaci, ko zamba ba a wurin aiki.