Jihohi kadan ne suka karbi tirela 20 na tallafin shinkafar da gwamnatin tarayya ta ware wa kowacce jihohi da ke fadin kasar nan, inda zuwa lokacin rubuta wannan labari aka shiga rudani ganin yadda wasu jihohi da dama tirelolin shinkafar ba su iso gare su ba.
Wani bincike da aka gudanar a karshen makon da ya gabata ya nuna cewa babu wata jihar arewa da ta samu shinkafar sai dai Jihar Kano, yayin da a yankin jihohin kudu maso yamma suka amshi nasu illa Oyo ce kawai ta yi ikirarin cewa motocin ba sun iso.
- Jihohi 11 Sun Kammala Jigilar Dawo Da AlhazansuÂ
- 2027: Fafutukar Jan Akalar Jam’iyyar PDP Ta Koma Jihohi
A jihohin kudu maso kudu, da suka hada da Akwa-Ibom, Ribas da Bayelsa jami’an sun tabbatar da samun tallafin, yayin da wasu suka ce ba su isa ba.
Gwamnatin Jihar Delta ta ce har zuwa ranar Juma’a ba a samu shinkafar ba, yayin da jami’an jihohin Edo da Kuros Ribas ba su amsa nasu ba.
A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta ce ta ware tireloli na shinkafa 740 ga jihohi 36 na tarayya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ana sa ran kowace jiha ciki har da Abuja za samu tiraloli guda 20 masu dauke da buhu shinkafa 1,200 na kilogiram 25 kowanne, sannan kuma za a raba shinkafar ga marasa galihu a cikin al’umma.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Abuja.
Ministan wanda ke tare da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce shugaban kasar ya umarci ministan noma da ya tabbatar an samar da abinci ga ‘yan Nijeriya.
Ya kuma bayyana cewa an raba tirelolin shinkafar ne don ganin an daidaita kuncin rayuwa da ake fama da su a kasar, yana mai cewa ana sa ran gwamnonin jihohin za su raba motocin ga marasa galihu.