Gwamnatin tarayya ta gargadi shuwagabannin kananan hukumomin kan al’mubazzaranci da kudin kananan hukumomi da gwamnatin tarayya za ta fara tura mu su kai tsaye.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi ya jaddada cewa shugabannin kananan hukumomi ba su da kariya, wanda hakan zai sa a kama su ko tuhumar su idan suka barnatar da kudin.
Fagbemi Ya nemi shuwagabbin kananan hukumomin da su mayar da hanakali wajen ayyukan raya kasa kamar gina tituna, samar da magudanun ruwa da kuma ayyukan jin kai na gaggawa ga wadanda suka gamu da ibti’la’i.
Ministan ya na wannan batun ne a wajen taron da kungiyar HURIWA ta shirya dan magance cin hanci da rashawa a bangarorin gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.
A wajen taron, Ko’odinetan HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya yi kira ga gwamnati da ta rage kudaden da ake amfani da su wajen gudanar da mulki wanda hakan ne zai taimaka wajen magance cin hanci da rashawa da kuma rashin ayyukan yi a tsakanin ‘yan Kasa