• English
  • Business News
Sunday, June 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsakanin Dangote Da Mahukuntan Fetur: Ina Muka Dosa?

by Abdulrazaq Yahuza
11 months ago
in Labarai, Manyan Labarai
0
Tsakanin Dangote Da Mahukuntan Fetur: Ina Muka Dosa?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kwanan nan, rikicin da ya barke na cacar baki tsakanin hamshakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote da mahukuntan bangaren mai na Nijeriya ya dauki hankali sosai a manyan gidajen jaridu da sauran kafofin sadarwa har da na sada zumunta.

Saboda mamakin abin, ‘yan Nijeriya masu kishi sun shiga rudani a kan rikicin. Da farko, attajirin ya zargi Kamfanonin Mai na Waje da ke aiki a Nijeriya da yi wa sabuwar matatarsa zagon kasa ta hanyar hana su samun danyen man da ake hakowa a Nijeriya da rahusa. Sai ma ya zama, yadda za a sayar wa wasu a waje ya fi nashi sauki, inda shi aka kara masa farashin daga dala 4 zuwa dala 6 a kan kowace ganga.

  • Majalisa Ta Nemi A Kori Shugaban Hukumar NMDPRA Kan Zargin Rashin Ingancin Matatar Dangote
  • Duk Da Sulhu, Tsugune Ba Ta Kare Ba Tsakanin Dangote Da Mahukuntan Mai

Uhum! In ji mai ciwon hakori. Cikakken Dan Nijeriya, ya kafa matatar mai a kasarsa ta gado amma an ki sayar masa da man kasarsa don ya tace ya sayar wa da ‘yan kasarsa. Wace irin kasa ce wannan? Kuma maimakon mahukuntan da abin ya shafa su nemi hanyoyin daidaita lamarin, sai suka zama masu mara baya ga kamfanonin na waje har ma suka fi su tsanantawa ta hanyar kushe sabuwar matatar man wacce babu irin ta kaf Afirka, alhali kuma sun ki gyara na kasa da ake da su guda uku a Kaduna, Warri da Fatakwal duk da makudan biliyoyin da aka narka.

Lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin mai, ya yi alkawari wa ‘yan kwadago cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a watan Disambar 2023. Aka ce ba a kammala aiki ba, amma a watan Janairun 2024 za ta fara, da watan ya zo ya shige sai aka kuma cewa babu shakka a watan Afrilu za ta fara, amma mai karatu har yau shiru kamar Malam ya ci shirwa. Kuma wani dan kasuwa shi kadai, ya bugi kirji, ya yi abin da kasar ta kasa yi, amma sai aka rika bin sa da tsangwama da hantara.

Kamar yadda na ji wani mai hikima yana jawabi a wani faifan bidiyo da na gani yana yawo a shafukan sada zumunta yana cewa, Nijeriya ta kasance tana sayar da danyen mai a kasashen waje daga nan sai ta sayo tataccen mai daga can. A yanzu kuma da aka samu matatar mai ta Dangote, sai aka hana matatar man isasshen danyen mai da za ta tace, don haka sai aka kuma garzayawa waje don shigo da danyen mai wadda daga bisani bayan tacewa za a kuma fitarwa zuwa waje. Wannan wane irin kwance zani ne a kasuwa?

Labarai Masu Nasaba

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

A duk kasashen Afira, kasashe biyu ne rak ba su shigo da tataccen mai daga waje. Daga Aljeriya sai Libiya, sannan kusan an kwashe shekara 20 kasar Angola tana fafutukar kafa babbar matatar mai abin bai yiwu ba, haka nan ita ma Yuganda ta kwashe shekaru 15, duk dai bai yiwu ba. To, mu me ya sa da namu ya yi maimakon a yaba sai aka koma bita-da-kulli?

Matatar man Dangote abar alfahari ce ga Nijeriya a tsakanin sa’o’inta na duniya. Saboda tun daga zayyanarta har zuwa gina ta da sanya na’urorin aiki komai a Nijeriya aka yi. Na ji cewa, Dangote ya yi wa katafaren gine-gine da ake ganin babu kamarsa a Nijeriya na Julius Berger tayin aikin amma kamfanin ya ce ba shi da kayan aikin da zai iya kwangilar. Dole ta sa Dangoten da kansa ya niki gari ya bazama neman kayan aikinsa da kansa kuma ya yi amfani da injiniyoyi na cikin gida masu yawa wajen aikin ginawa.

Dangote

Kamar yadda mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Mista Edwin ya tabbatar, wannan ne karon farko da aka samu katafariyar matatar mai da za ta tace ganga 650,000 a kullum da aka hada kwangilar sauton kayan aiki da kawo su da kuma gina su a lokaci guda a duk fadin duniya kuma irin ta, ta uku da ta hade sassan matatar mai a wuri daya a duk fadin duniya. Wannan kadai bai ishe mu alfahari ba? Sannan Bisa kayan aikin da aka shigo da su na gina matatar, Dangote ya ce babu wani aikin gini da zai iya gagarar Nijeriya a halin yanzu.

Shugaban Hukumar Daidata Al’amuran Mai ta Kasa, Injiniya Faruk Ahmed ya yi zargin Dangote yana yunkuri ne na yin babakere a harkar man Nijeriya, to amma Dangoten ya ba shi amsar cewa, “ba mu taba ko da darsawa a zuciya cewa, mu hana wani yin kasuwancin da muke yi ba. Duk wanda zai yi ai ga fili ga doki.”

Kuma ma don Allah, don dan kasa ya gina wani abu na samun kudi a kasarsa ta gado mene ne na kyashi? Ai da arziki a garin wasu gwara a naku. Amma a wurin shugabannin mai na Nijeriya gwara a bai wa turawan yamma. Shi ya sa wani ya ce, “da zarar wani ya yi maka bayani a game da yadda za ka fahimci Nijeriya, bayan ya kammala sai ka ce ka gane, to tabbas bai yi maka bayani yadda ya kamata ba ne,” ma’ana, duk yadda aka kai ga yi maka bayani, za ka rasa INA MUKA DOSA?

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: DangoteFetur
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Shiga Rudani Saboda Rashin Isar Tirelolin Shinkafar Tallafi Wasu Jihohi

Next Post

Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars 

Related

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki
Manyan Labarai

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

31 minutes ago
Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 46.25
Labarai

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

15 hours ago
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
Manyan Labarai

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

15 hours ago
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)
Labarai

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

16 hours ago
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe
Manyan Labarai

Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku

17 hours ago
Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu
Manyan Labarai

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

19 hours ago
Next Post
Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars 

Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars 

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

June 29, 2025
Kasar Sin Ta Sake Ware Yuan Miliyan 100 Domin Tallafawa Lardin Guizhou Dake Fama Da Ambaliya 

Kasar Sin Ta Sake Ware Yuan Miliyan 100 Domin Tallafawa Lardin Guizhou Dake Fama Da Ambaliya 

June 28, 2025
An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin

An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin

June 28, 2025
Jakadun Kasa Da Kasa Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwa Wajen Amfani Da Makamashin Nukiliya Ta Hanyar Lumana

Jakadun Kasa Da Kasa Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwa Wajen Amfani Da Makamashin Nukiliya Ta Hanyar Lumana

June 28, 2025
Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa

Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa

June 28, 2025
Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 46.25

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

June 28, 2025
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

June 28, 2025
Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025

Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025

June 28, 2025
An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

June 28, 2025
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

June 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.