Yau Litinin 29 ga watan nan, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, da hukumar kula da yawon bude ido ta MDD, wato “UN Tourism” sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a birnin Madrid na kasar Sifaniya, inda suka cimma matsayi daya kan hadin gwiwa a fannonin da suka hada da bayar da labaran al’adu da yawon bude ido, da tallata alamun yawon bude ido, da ma shirya ayyukan kafofin watsa labaru da dai sauransu. Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban CMG Shen Haixiong, ya shaida hakan tare da madam Zoritsa Urosevic, darektar zartarwa ta “UN Tourism”.
Mista Shen Haixiong ya ce, kudurin da aka dudduba tare da zartas da shi a yayin cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 da ya gudana a kwanakin baya, wanda ya shafi kara zurfafa yin gyare-gyare a dukkan fannoni, da kuma inganta zamanintarwa iri na kasar Sin, ya hada da ayoyi 60, masu kunshe da matakan yin gyare-gyare sama da 300, wadanda yawancinsu ke da alaka da al’adu da yawon bude ido.
- Magajin Garin Birnin Madrid Ya Zanta Da Shugaban CMG
- NCC Ta Umarci Kamfanonin Sadarwa Su Gaggauta Sake Haɗa Layukan Wayar Da Aka Katse Saboda NIN-SIM
A cewarsa, zurfafa hadin kai a tsakanin kafofin watsa labaru, da masu kula da yawon shakatawa yana da makoma mai kyau. CMG a shirye yake ya dauki wannan bikin rattaba hannu a matsayin wata dama ta inganta hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, a fannonin tsare-tsare, da samar da bayanai da watsa shirye-shirye da dai sauransu, da kuma zama amintacciyar abokiyar “UN Tourism”, wajen inganta mu’amalar yawon bude ido a tsakanin kasashe daban daban.
A nata bangare, madam Urosevic ta ce, kasar Sin muhimmiyar mamba ce ta “UN Tourism”. Kana ta bayyana fatanta na ganin an zurfafa hadin gwiwa a tsakanin hukumarta da CMG a fannoni da dama a nan gaba, tare da tsara sabon nau’in sana’ar yawon shakatawa, da habaka sana’ar yawon bude ido don zama mai dorewa, da hakuri da juna da kuma juriya. (Bilkisu Xin)