Gasar wasannin Olympics ta dade da sauya manufarta ta zakulo mafi kyawun ‘yan wasa a duniya, yanzu ta zama dandalin cudanyar bil’adama, bege da mafarkai, da zaman lafiya da hadin kai. Wasanni gaba daya, musamman wasannin Olympics, na hada kan jama’a ba tare da la’akari da bambancin matsayi na shugabanci, ko siyasa ko addini ba. A kan samu hayaniyar farin ciki da jin dadin yayin da ‘yan wasa suka hadu a waje guda, suna cike da shauki da kishi tare da alfahari a matsayin wakilan duniya yayin da tutocin kasashensu ke shawagi a barandun wuraren da aka ajiye su.
Duk da cewa dukkansu suna da gagarumin aiki a gabansu, wato aikin atisaye, horo da gasa, hakan ba ya hana su samun lokacin yin musaya da mu’amalar cudanya tsakanin juna, musamman idan sun taba haduwa a fagen wasa, kuma cikin farin ciki za ka ga suna daukar hoto da musayar bayanan tuntubar juna. Wadannan ‘yan wasa sun zama abokai na dindindin kuma suna iya ba da gudummawa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin kasashe a nan gaba.
- Zanga-Zanga: Sojoji Sun Karɓe Iko Da Tsaron Hanyar Shiga Abuja
- Magajin Garin Birnin Madrid Ya Zanta Da Shugaban CMG
Yayin da al’ummar duniya ta yi dafifi a birnin Paris don halartar gasar wasannin Olympics na lokacin zafi karo na 33, mun ga yadda ’yan wasa daga kasashen da a halin yanzu ke yakar juna, suke mu’amalantar juna cikin farin ciki, alal misali, mun ga ’yan wasa daga Ukraine da Rasha da Belarus suna fafatawa a matsayinsu na ’yan wasa ba tare da la’akari da yakin da ake gwabzawa a Ukraine ba. Ga kasar Afganistan, duk da cewa mata na fuskantar kalubale a wasu fannoni musamman a fannin wasannin motsa jiki.
Amma duk da haka, sakamakon kokarin kungiyoyin wasanni na kasa da kasa, irinsu kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, da kwamitin Olympics na Asiya (OCA), wasu mata uku na kasar Afghanistan suna wakiltar kasarsu a birnin Paris, tare da maza uku.
Wannan yana wakiltar babban nasara ga al’ummar duniya kuma yana jaddada karfin ikon wasanni wajen hada kan duniya.
Wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008 ya kasance misali mafi kyau, yayin da aka gabatar wa duniyar masu kallo kasar Sin na zamani kuma mai fa’ida cike kuzari, kuma dimbin mutane suka samu karin haske game da tarihi da al’adun da ci gaban kasar Sin ta hanyar yawon bude ido da shakatawa.