A karshen watan Yulin bana, an yi sabon zagayen shawarwarin “2+2”, wato shawarwarin ministocin harkokin waje, da na ministocin tsaron gida, tsakanin kasashen Philippines da Amurka, al’amarin da ya kasance karo na farko tun shekara ta 2013, da Philippines ta gudanar da shawarwarin nan. Kafin wannan, kasar Sin da kasar Philippines sun cimma ra’ayi daya na wucin-gadi domin shawo kan halin karamin tsibirin Ren’ai Jiao, abun ya kawo kwanciyar hankali na wani kankanin lokaci ga rikicin tekun kudancin kasar Sin.
Amma ga ita Amurka, ko kadan ba ta son ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a tekun kudancin kasar Sin. Alal misali, a wajen sanarwar da Philippines da Amurka suka bayar cikin hadin-gwiwa a wannan karo, Amurka ta jaddada alkawarin da ta yi wa Philippines a fannin tsaro. Kana, bayan shawarwarin, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya sanar da cewa, kasarsa za ta baiwa Philippines tallafin dala miliyan 500, don taimaka mata inganta kwarewar tsaron gida.
- Wang Yi Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Zambiya
- Sin Ta Kashe Yuan Biliyan 300 A Aikin Gina Tituna A Xizang A Tsakanin Shekarar 1953-2023
Shaidu sun tabbatar da cewa, Amurka ce dalili mafi girma, da zai iya haifar da abubuwan rashin sanin tabbas ga manufofin Philippines kan kasar Sin, da wadanda suka shafi tekun kudancin kasar Sin.
Ya kamata wasu ’yan siyasar Philippines su gane cewa, alkawarin da Amurka ta yiwa kasar su a bangaren tsaro, ba zai haifar da da mai ido ba, kana, ainihin makasudin kulla kawance tsakanin Amurka da Philippines, shi ne taimakwa Amurkar nuna babakere a duniya. Philippines ba ta Amurka ce ba, ta Asiya ce. Don haka, dole ta yi taka-tsantsan da kara yin tunani mai kyau game da kyautar da Amurka ta ba ta, kuma ya kamata ta maida hankali kan yankin da take ciki, da kulla zumunta da kasashe makwabtanta, a yayin da take tsara manufofin diflomasiyyarta. (Murtala Zhang)