Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin Inuwar Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya yi Allah wadai da amfani da harsashi kan ‘yan kasar da ke zanga-zangar lumana kan matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.
Atiku ya yi wannan kakkausar lafazi ne yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a Nijeriya inda wasu jihohi aka samu hargitsi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar kamar Kano da Abuja.
- Yanzu Ne Lokacin Da Ya Dace Arsenal Ta Lashe Kofin Firimiya – Kroenke
- Gwamnatin Kano Ta Sassauta Dokar Hana Fita
Zanga-zangar wacce aka shirya gudanarwa daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta, an samu rahotannin asarar rayuka, lalatawa tare da wawure dukiyar gwamnati da al’ummar kasa a wasu jihohin kasar.
Atiku ya bayyana matakin jami’an tsaro na yin amfani da harsashi akan masu zanga-zangar da cewa, “abu ne mai muni da ya yi kama da zamanin mulkin kama-karya na soji.”
Ya kara da cewa, “Yana da matukar muhimmanci a tunatar da gwamnati da hukumomin tsaro babban hakkin da ya rataya akansu na tabbatar da tsaro ta yadda ‘yan kasa za su iya amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zanga ba tare da tsoro ba.
“Duk lokacin da jami’an tsaro suka bude wuta kan masu zanga-zangar lumana, babu abinda zai biyo baya face kara ta’azzarar hargitsi.
“Ina kira ga kasashen duniya da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da su sanya ido sosai kan al’amuran da ke faruwa a Nijeriya.
“Ina sake jaddada shawarara ga masu zanga-zangar da su dage da yin amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zangar lumana tare da yin watsi da duk wani nau’i na tashin hankali.
“Amma ya zama dole a gurfanar da masu wawure dukiyar jama’a da barnata kadarorin gwamnati a gaban kotu kamar yadda doka ta tanada, don irin waɗannan ayyukan, suna lalata halaccin zanga-zangar.
“Dole ne Shugaba Tinubu ya nuna jagoranci na gaskiya ta hanyar yin gaggawa da aiwatar da bukatun al’ummar Nijeriya.”