Kwamitin tsaro na jihar Kaduna ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a cikin garin Kaduna da Zariya. Hukuncin kuma ya fara aiki nan take.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin.
- Hukumar SEMA Ta Jihar Kebbi Ta Tallafa Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwan Sama Ta Shafa A Argungu
- Gwamnan Filato Ya Ƙaƙaba Dokar Hana Fita Ta Awa 24
“Majalisar tsaro ta jihar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, bayan ta duba yanayin tsaro a jihar, ta na sanar da ‘yan jihar Kaduna cewa:
“Akwai isassun hujjoji da ke nuna wa karara cewa, zanga-zangar da ake ci gaba da yi, wasu bata-gari sun mamaye ta inda suka fara lalata dukiyoyin jama’a.
“Saboda wannan abin takaici, Majalisar Tsaro ta Jihar Kaduna, ta yanke shawarar kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garuruwan Kaduna da Zariya da kewaye, nan take.
”An shawarci mazauna jihar da su kasance a cikin gida yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin tabbatar da tsaro.” In ji sanarwar