Kasar Sin ta ba da gudunmuwar dala miliyan 3 ga hukumar kula da agajin jin kai ga Palasdinawa ‘yan gudun hijira ta MDD (UNRWA), domin tallafawa agajin jin kai a yankin Gaza.
Shugaban ofishin kula da harkokin Palasdinu na kasar Sin Zeng Jixin ne ya rattaba hannu kan yarjejeniyar bayar da gudunmuwar, tare da babbar kwamishina mai kula da ayyukan hukumar UNRWA, Antonia Marie De Meo.
- Jami’in Zimbabwe Ya Yabawa Kamfanin Kasar Sin Da Ya Goyi Bayan Ajandar Bunkasa Masana’antun SADC
- Yarjejeniyar Beijing: Mabudin Zaman Lafiya A Zirin Gaza
A cewar Zeng Jixin, kasar Sin ta kasance mai taimakawa ayyukan UNRWA wajen sauke nauyin dake wuyanta, kuma tana kira ga kasashen duniya su ma su taimakawa ayyukan hukumar. Ya kara da cewa, ko a bara bayan barkewar rikici a Gaza, kasar Sin ta samar da gudunmuwar kudi ga hukumar cikin gaggawa.
Bugu da kari, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da shawarar tabbatar da tsaro a duniya, da hada hannu da kasa da kasa wajen kawo karshen rikicin Gaza nan ba da jimawa ba, da saukaka yanayin jin kai a yankin da ganin an aiwatar da manufar kafa kasashe biyu.
A madadin hukumar UNRWA, De Meo ta bayyana godiya ga taimakon da kasar Sin ke ba hukumar a kai a kai, tana mai cewa, gudunmuwar ta Sin na da muhimmanci matuka. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)