Duk da dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa a garin Jos da Bukuru na Jihar Filato, matasan yankin Dilimi da ke Jos ta Arewa sun bijirewa matakan tsaro, lamarin da ya haifar da taho mu gama.
Lamarin dai ya ta’azzara ne a lokacin da matasan suka fito da yawansu domin tunkarar wasu shaguna da ke wurin, wanda hakan ya haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro da aka girke domin tabbatar da doka da oda.
Ya zuwa lokacin cika wannan rahoto, ana jin ƙarar harbe-harbe a yankin inda jami’an tsaro suka dukufa wajen ganin an shawo kan lamarin tare da tabbatar da zaman lafiya.
Idan dai za a iya tunawa a daren jiya ne gwamnatin jihar Filato, ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Jos da Bukuru domin tabbatar da doka da oda ganin yadda ake gudanar da zanga-zangar a fadin ƙasar nan da kuma yadda ɓata gari ke sata da suna zanga-zangar.