Rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Laraba ta yi gargadin cewa bata-gari sun shiga cikin masu zanga-zangar #EndBadGovenance a jihar.
Ta nuna damuwa kan lamarin tare da bayyana cewa, rundunar na aiwatar da matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya.
- ’Yansanda Sun Cafke Karin Mutane 82 Kan Zanga-zangar Yunwa A Jigawa
- Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki
“Zanga-zangar da ke gudana a Ribas ta rikide zuwa hargitsi, inda bata-gari ke muzgunawa masu gudanar da kasuwanci da ayyukan yau da kullum.
“Suna kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa, suna tilasta wa masu ababen hawa cewa, dole su dora ganye a kan ababen hawansu, suna tare manyan tituna, suna lalata allunan talla, da kuma barazana ga ‘yan kasuwa.
“Masu zanga-zangar sun kuma kona tayoyi a kan tituna”, in ji ta.
Kakakin rundunar ta kara da cewa, zanga-zangar na sake sabon fasali.