A ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta ne; aka fara zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa da matsalar tsaro da kuma neman samun shugabanci nagari a fadin Nijeriya.
Duk da kokarin bangaren gwamnati da shugabannin al’umma da na addini da sauran masu ruwa da tsaki na lallashi har ma da tabbaci na bin matakan shawo kan matsalolin tsadar rayuwa, domin dakatar da zanga-zangar ta kwana 10, wadanda suka shirya sun yi kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen da aka yi musu na dakatarwa.
- Shugaban Zanzibar Ta Tanzania: Ba Za Iya Raba Ci Gaban Afirka Da Sin Ba
- Firaministan Pakistan: Bunkasuwar Sin Ya Zama Abin Misali Ga Kasar
Da farko dai zanga-zangar, wadda aka shirya ta lumana ta fara wakana ce a jihohi da dama cikin kwanciyar hankali, amma daga bisani ta rikide a wasu wuraren zuwa tashin hankali.
Ma’aikatu da hukumomin gwamnati da bankuna da sauran gine-gine na gwamnati da harkokin kasuwanci, sun kasance a rufe a jihohi da dama.
A Jihohin Kaduna da Kano da Jigawa da Borno da Bauchi, Filato da kuma Katsina; zanga-zangar ta rikide ta koma tarzoma, inda wasu gungun matasa suka fara afka wa ma’aikatun gwamnati da shagunan ‘yan kasuwa, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, lamarin da ya kara munana zanga-zangar.
Wanna ya sa al’umma suka fara tunanin shin riba aka kirga ko kuma asara?
Zanga-zangar ta yi matukar daukar hankalin jama’a tare da sanya fargaba a zukatansu; musamman ganin yadda masu yi suka rika farfasa shagunan mutane da konawa tare da fasa ma’aikatun gwamnati da yin artabu tsakaninsu da kuma jami’an tsaro.
Daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali, akwai kwace wata motar yaki ta ‘yansanda da kuma daga tutar kasar Rasha tare da ambaton neman Shugaba Putin ya kawo musu dauki da aka zargi masu zanga-zangar da yi.
Masana tattalin arzikin kasa daban-daban sun hasashen an tafka mummunar asarar dukiya don haka suke ganin maimakon a samu mafita sai kuma hannun agogo ya koma baya.
Kaduna
A Jihar Kaduna, zanga-zangar ta rikide ta koma tarzoma, lamarin da ya kai ga rasa rayuka da barnata kayan gwamnati da wasu bankuna da kuma kwacen waya.
Tun da farko dai, matasan da suka fara yin gangami; sun taso ne daga Gadar Kawo, wasu kuma daga unguwannin Tudun wada da Rigasa, inda suka nufi gidan gwamnatin jihar. Kazalika, bata-garin sun rika aikata miyagun abubuwa da suka hada da kwacen waya a hannun jama’a.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wasu daga cikin gungun matasan; sun fasa wani gida a kusa da Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna da kuma wani gidan burodi, inda suka rika kwasar taliya da man girki a jarkoki duk da cewa; a makon da ya gabata sun fasa tare da kona hedikwatar hukumar kula da abeben hawa ta jihar tare da kwashe kayan ciki da kuma kona ginin hukumar.
Haka zalika, matasan sun shiga bankin Fidelity da ke Tudun Wada, inda suka fasa wurin na’urar cire kudi ta ATM, suka daka wa kudaden ciki wawa.
Hasali ma, wasu daga cikin matasan sun rika balle duk wani abu da suka gani na karfe da cire fitilun kan titi masu amfani da hasken rana, yayin da kuma suka cinna wa tayoyi wuta; don su kashe hanya.
Amma daga bisani, jami’an tsaro sun rika bi suna kama wadannan matasa da suka yi amfani da sunan zanga-zanga; suna sace kayayyakin al’umma.
Jim kadan bayan faruwar lamarin, Gwamnan Jihar Kaduna; Sanata Uba Sani ya bayyana takaicinsa dangane da yadda bata-garin suka barnatar da dukiyar al’umma da kuma na gwamnati.
A zantawarsa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar, Gwamna Uba Sani ya ce, “Babban takaicina shi ne, yadda aka barnatar da kayan jama’a; musamman wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba.
“Bata-gari ko in ce barayi ne suka fito suka fasa ofisoshin gwamnati guda biyu, suka kuma fasa gidan wata mata tare da kwashe mata kaya, wannan ko shakka babu abin takaici ne kwarai da gaske, saboda ko kadan bai kamata a ce al’ummar da suka fito neman na kansu; haka kawai a zo a barnatar musu da dukiyoyinsu babu kaira babu dalili ba, wannan abin takaici ne matuka.
“Gudanar da zanga-zangar ba matsala ba ce, amma yadda muka ga wasu matasa bata-gari suka kwace zanga-zangar tare da yin amfani da ita wajen sace kayan mutane, hakan ya sa dole muka dauki matakin tsaro; domin dakile zanga-zangar. ”
Uba Sani ya kara da cewa, an tafka asara mai yawan gaske a cikin garin Kaduna na barnata kayan gwamnati da na daidaikun mutane.
A wata zantawa da ya yi da wakilinmu, Shugaban Kungiyar Sufuri ta Kasa (NURTW) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya bayyana cewa, ganin yadda zanga-zangar ta dauki sabon salo, hakan ya sanya suka dauki matakan kare daukacin tashoshin motoci da ke Kaduna; domin kauce wa bata-gari masu fakewa da zanga-zangar suna barnata kayan al’umma.
Alhaji Aliyu, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kungiyar sufuri ta kasa mai kula da shiyyar Arewa maso yamma ya ce; tun da aka fara wannan zanga-zangar, babu wani direba da ya shiga cikinta.
Ya yi kira ga daukacin direbobin sufuri da su zama masu bin doka da oda a daidai lokacin kana ya ce tun lokacin da aka fara gudanar da zanga-zangar ba su samu rahoton rasa rai ko dukiyar wani direba ba, inda ya kara jaddada umarnin kungiyar na kauce wa shiga duk wata zanga-zanga.
Shi ma Babban Daraktan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar, Dakta Maina Abdullahi Isma’ila Gimba ya ce, dama tun farko sun hangi cewa zanga- zangar ba za ta haifar da da mai ido ba kuma hakan ta faru.
Ya ce, zanga-zangar a jihar ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyin jama’a maimakon samun nasara.
“Tun da aka fara wannan zanga-zanga, duk asibitoci a rufe suke; ma’aikatun gwamnati su ma a rufe, haka nan ma bankuna, uwa uba kuma ga asarar rayuwa da aka tafka, saboda haka; wannan zanga-zanga ba ta haifar da komai ba illa asara.
“Muna kira ga shugabanni, kama daga shugaban kasa zuwa gwamnoni da su duba halin da ake ciki a wannan kasa na kuncin rayuwa; su sassauta lamura don talaka ya samu saukin rayuwa, wanda tsadar rayuwar ce ta jawo wannan asarar da aka yi.” In ji shi.
A ziyara da wakilinmu ya kai wasu unguwannin da ke kwaryar cikin garin Kaduna, ‘yan kasuwa da direbobin sufuri sun bayyana cewa, zanga-zangar ta haifar musu da babban gibi, inda suka ce zanga-zangar ta sanya sun rufe shaguna tare da barin motocinsu a gida; domin kauce wa shiga hannun bata-gari masu fakewa da zanga- zangar suna satar kayan mutane.
Kano
Jihar Kano na cikin jihohin da zanga-zangar lumanar ta juye zuwa wasoson dukiyar al’umma tare da afka wa kadarorin gwamnati. Hakan ya jawo wasu hasalallun matasa suka shiga amfani da zanga-zangar wajen wawashe dukiyar al’ummar da kuma sake dawo da harkar fadace-fadacen ‘yan daba, wanda zuwa lokacin hada wannan rahoto akwai majiyoyi da suka tabbatar da asarar rayuka.
A ranar Alhamis, wadda ita ce ranar da aka fara tsunduma wannan zanga-zangar lumana, tun farar safiya aka fara hangen dandazon matasa dauke da kwalaye, wasu kuma na dauke da muggan makamai, inda suka fantsama tituna tare da fara kona tayoyi a kan mayan tituna.
Masu zanga-zangar, sun afka wa sakatariyar Audu Bako da kuma Hukumar Shari’a ta Jihar Kano; inda suka yi kaca-kaca da ita. Har masallacin da ke harabar kotun ma bai tsira ba, domin masu zanga-zangar sun wawashe komai a wannan masalaci; kama daga lasifika, shimfidar sallah, alkur’anai da sauransu duk ba su tsira ba, sannan suka shiga cikin ma’aikatar suka farfasa kayayyaki tare da kwashe na’urorin sanyaya daki( A/C) da kuma dukkanin sauran wani abu mai amfani.
Bayan zanga-zangar ta fara zafi ce, wasu gungun matasa suka kama hanyar zuwa Fadar Gwamnatin Kano da sunan kai kokensu ga gwamna, amma a kan hanyar tasu ta zuwa gidan gwamnatin, sai suka afka wa katafariyar cibiyar horar da matasa sana’o’in zamani ta Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), inda suka farfasa wannan cibiya tare da wawashe dukkanin abubuwan da suka samu a ciki; kama daga kan kwamfutoci da sauran abubuwan amfani.
Haka nan, shi ma wurin sayar da kayan taba-ka-lashe mai suna Barakat da ke kan titin zuwa Fadar Gwamnatin Kano bai tsira ba, domin kuwa an farfasa shi tare da kwashe kayan da ake sayarwa a ciki.
Al’ummar yankin unguwannin Kurna da na Rijiyar lemo, sun zargi wani dansanda da laifin kashe mutane masu yawa a cikin masu zanga-zangar a tsakanin unguwannin biyu, kamar yadda wani faifan bidiyo ya karade kafafen sadarwa na zamani, inda aka nuna hoton dansandan sanye da hirami; wanda aka ce dama bai fiya sa hular aiki ba. Sai dai, rudunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa; tana gudanar da bincike kan lamarin.
Wani abin mamaki shi ne, wani matashi da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa, ya yi cinikin babur tare da yin alkawarin biyan kudi idan ya dawo daga zanga-zangar. Ya ce, tuni ya kammala hangen inda za su tunkara wajen dibar ‘ganima’.
Zanga-zangar dai ta fi zafi tare da tafka ta’asa a unguwannin Sheka, Medile, Rijiyar lemo da kuma wasu sassan na Jihar Kano.
A rana ta hudu da tsunduma zanga-zangar, kwatsam sai aka hangi dandazon matasa dauke da tutocin kasar Rasha, inda suke nuna goyan bayansu ga kasar tare da kiran kawo musu dauki a kan halin ko-in-kula na shugabannin gwamnatin Nijeriya, har ma wasu daga cikin masu zanga-zangar na shelanta zabar komawa karkashin mulkin soja; domin bakanta ran gwamnati mai ci da ‘yan kanzanginta.
Wani mazaunin Unguwar Rijiyar Lemo, mai suna Abubakar Musa ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa, wasu gungun matasa ne suka fito zanga-zanga kan titi suna nuna rashin amincewarsu da gwamnatin, duk da cewa an sanya dokar hana zirga-zirga, lamarin da haifar da arangama tsakaninsu da jami’an tsaro.
“A gabana mutane takwas suka mutu, maza da mata da yara lokacin da jami’an tsaro ke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar.”
Ya ce, babban kantin sayar da fura da nono na Rufaida da ke Rijiyar Lemo; bata-garin sun fasa shi tare da kwashe komai da ke cikin kantin, lamarin da ya kai ga hatta babban jami’in ‘yansanda (DOP) na yankin; matasan sun raunata shi.
Katsina
A garin Daura na Jihar Katsina kuwa, wasu bata-gari ne da suka fake da zanga-zangar suka kai farmaki wani coci mai suna ‘Libing Faith’ a ranar Lahadi, inda suka yi awon gaba da kujeru akalla 205 da kayan kade-kade da kuma wasu kayayyaki masu daraja na miliyoyin naira.
Faston cocin ya ce, duk da kasancewar suna da jami’an tsaro guda biyu da ke aiki a nan, amma masu zanga-zangar ba su ji shakkar far musu ba.
Ya nunar da cewa; masu zanga-zangar sun karkatar da ita zuwa wani abu daban, inda suka karya kofa da ajujuwa suka kutsa cikin cocin tare da ci gaba da yin sace-sace.
A cewarsa, sun kwashe komai na cikin cocin, ciki har da agogon bango, kayan kida, kujerun limaman coci da kuma na’urar kwamfuta da sauran makamantansu.
Bauchi
A Jihar Bauchi dai, tun ranar farko na zanga-zangar matsin rayuwar da matasa suka fito a cikin garin da wasu kananan hukumomi an samu kai ruwa rana tsakanin matasan da jami’an tsaro, musamman a daidai shatale-talen CBN, yayin da masu zanga-zangar suka yi yunkuri wucewa zuwa gidan gwamnatin jihar domin bayyana damuwarsu.
Lamarin dai ya kai ga harba barkonan tsohowa da tarwatsa masu zanga-zangar. An samu rahoton zargin wasu ‘yansanda da lakada duka ga wani nakasasshe, Hamza Waziri a kofar gidan gwamnatin jihar.
An ga Hamza a wani faifayin bidiyo yadda ya sha duka a hannun ‘yansanda yayin da yake kan keken guragu. Ko da yake nan take gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ba da umarnin kaddamar da bincike kan lamarin.
Har ila yau, wata mata mai suna Aisha Dogara ta yi zargin cewa wani dansanda ya mata duka a kokarinta na zuwa gidan gwamnatin jihar.
Kazalika, a ranar Litinin matasan da ke zanga-zangar sun kutsa kai cikin gidan gwamnatin Jihar Bauchi da ke garin Azare shalkwatar karamar hukumar Katagum, gami da gidan tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, inda suka wawushe komai.
Har ila yau, masu zanga-zangar sun banka wuta ga wani bangaren sakatariyar karamar hukumar Katagum, inda suka lalata manyan ofisoshi kusan goma da kona muhimman takardu.
Wannan ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a karamar hukumar Katagum ta awa 24, amma daga baya an sassauta zuwa awa 12.
Wasu mazauna Azare sun tabbatar wa majiyarmu cewa akwai mutane akalla uku da suka samu raunin harbin bindiga a yayin arangama da jami’an tsaro, haka kuma; sun tabbatar da daga tutocin kasar Rasha a lokacin zanga-zangar.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Awwal Musa Muhammad ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya ce, “Mutane sun fito zanga-zangar da yawan gaske, sai kuma suka fara lalata kayan jama’a kamar sakatariyar karamar hukuma, inda suka cinna mata wuta, amma Allah ya taimake mu ba su kona ta baki-daya ba.”
Kwamishinan ‘yansandan ya kara da cewa, sun kuma kai hari gidan gwamnatin jihar da ke Azare, inda suka soma ciccire kayayyaki kafin jami’an tsaro su tarwatsa su tare kuma da kwace wasu kayayyakin da suka soma wawushewa.
Zuwa rubuta rahoton nan dai hankula sun kwanta aJihar Bauchi tun lokacin da Gwamna Bala Muhamma ya kira taron mambobin majalisar tsaro tare da rokon matasa da su janye zanga-zangar.
Gombe
A Jihar Gombe kuma, tun a ranar farko ta zanga-zangar aka samu barnata kadarori da tashin-ashina.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, a ranar Litinin ya jagoranci wani babban taron gaggawa na majalisar tsaro don duba halin da ake ciki tare da samar da tsarin hadin gwiwa don magance sake aukuwar lamarin.
Babban taron wanda ya hada da shugabannin hukumomin tsaro, da kwamishinoni masu nasaba da abin, da shugabannin kananan hukumomi da sarakunan gargajiya, ya mayar da hankali ne kan yanayin tsaron jihar bayan zanga-zangar, da kuma daukar matakan magance aukuwar hakan a nan gaba tare da tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, tare da kwamishinan ‘yansanda CP Hayatu Usman da sauran shugabannin hukumomin tsaro, sun yi bayani ga manema labarai.
Sakataren ya ce, “Gwamnati ta fahimci cewa matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita ce ta janyo zanga-zangar, mun damu matuka don kyautata jin dadin al’ummarmu, kuma mun himmatu wajen magance wadannan matsalolin cikin gaggawa, mun yarda cewa tsaro abu ne da ya shafi kowa, don haka muna kira ga jama’a su ci gaba da mara wa gwamnati da jami’an tsaro baya wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
“A wani bangare na sabon yunkurin da gwamnati ke yi na magance matsalolin, ta yi shirin sake raba tallafin abinci don tallafa wa marasa galihu a fadin jihar. Wannan yunkuri shi ne karo na 19 a cikin jerin tallafin da wannan gwamnatin ke yi, kuma za a yi shi ne da nufin ba da agajin gaggawa don tabbatar da cewa babu wani dan Jihar Gombe da ke fama da yunwa a wannan mawuyacin lokaci,” in ji sakataren.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Hayatu Usman wanda ya yi magana a madadin hukumomin tsaro, inda ya jaddada kudirin jami’an tsaro na tabbatar da doka da oda, tare da bai wa jama’a tabbacin tsaron lafiya da dukiyoyinsu, yana mai kira ga jama’a su kwantar da hankalunsu. Ya kuma jaddada cewa jami’an tsaro suna cikin shirin ko ta-kwana don dakile duk wata barazana tare da tabbatar da doka da oda.
Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kama mutane da dama dangane da wawure dukiyoyin gwamnati da na jama’a a yayin zanga-zangar, inda ya bayyana cewa an kwato wasu muhimman kayayyaki. Ya kuma bukaci wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu su je hedkwatar ‘yansandan jihar don tantance ko kayayyakinsu na cikin wadanda aka kwato don mika musu su cikin gaggawa.
Tsokacin Sufeto Janar Na ‘Yansanda Da Asarar Rayuka
Babban Sufeton Rundunar ‘Yansandan Nijeriya ya bayyana cewa, babu wani jami’insu da ya yi harbi a lokacin zanga-zangar matsin rayuwar da ya wakana a fadin kasar.
Babban sufeton, ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake kare zargin da aka yi wa jami’ansu sun nuna karfi fiye da kima, a yayin gudanar da taron manema labarai da Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, Janar Christpher Musa ya kira a Abuja, ranar Talata.
Ya ce, duk jami’in da aka gani da bakin kaki a ranar zanga-zangar ba jami’insu ba ne, saboda ba kayan da suka saba sanyawa suka sa a ranar ba.
Duk da ikirarin shugaban ‘yansandan cewa, jami’an tsaro ba su yi harbi kan masu zanga-zangar ba, akwai zarge-zarge masu karfi a kan jami’an tsaron na kashe wasu matasa hudu ciki har da wata budurwa mai suna Firdausi Muhammad da ake shirin yi mata aure wacce alburushin da aka harba ya yi ajalinta a Kano.
Haka nan, a ranar Talata an zargi wani soja da bindige wani matashi mai suna Isma’il Muhammad, dan shekaru 18 a unguwar Samaru da ke Zariya cikin Jihar Kaduna.
Bugu da kari, an kashe wani matashi daga cikin masu zanga-zangar mai suna Abdulkadir Labaran Babah Alfindiki a Kofar Nassarawa.
Da take zantawa da Daily Trust, mahaifiyarsa, Aisha Isah Babah ta ce, “Yarona ya bar gida ne domin zuwa wurin kasuwancinsa. Na kasance cikin damuwa da ban ga ya zo cin abincin rana ba a gida. Ban kira shi ba kuma ban yi magana da kowa game da lamarin, ban sani ba ma ashe an kashe shi.”
Ta ce, ta bar wa Allah komai kasancewar marigayin maraya ne kuma ba za ta iya bi musu hakkinsa ba.
Bugiu da kari, mahaifiyar wani matashi mai suna Kashifu Abdullahi Gyaranya dan shekara 15, wanda shi ma aka kashe a yayin zanga-zangar, Maryam Sani ta ce, “A lokacin da ya bar gida, na tambaye shi inda zai je; ya ce min zai je wurin abokinsa ne. Na gargade shi kar ya shiga zanga-zangar, ya ce ba zai shiga ba. Sai kawai kira na aka yi aka sanar da ni cewa, an kashe shi; daga nan kuma shi kenan.”
Haka kuma an ce, an kashe wani Umar Abubakar Hausawa da harsashi; wanda shi ma ake zargin ‘yansanda ne suka harbe shi a yayin zanga-zangar a Kofar Nassarawa duk dai a ranar.
Da yake mayar da martini kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na ‘yansandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce; ‘yansandan sun yi kokarin tabbatar da doka da oda ne a Rijiyar Lemo, yayin da matasan yankin suka yi kokarin cin galaba a kansu.
“A gaskiya abin da ya faru shi ne, kun san Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar hana fita a jihar, don hana matasan kutsawa cikin shagunan mutane su sace musu kaya. Don haka, mutanenmu suka yi kokarin tarwatsa su; amma maimakon su koma gidajensu sai suka juya lamarin zuwa tarzoma tare da fara jifan jami’anmu”.
Ya kara da cewa, lamarin ya sa aka kara karfafa ma’aikata; domin tabbatar da doka da oda.
Ya ci gaba da cewa, doka ta bai wa ‘yansanda damar kare kansu; sannan rundunar ta kaddamar da bincike kan lamarin, domin sanin ainahin abin da ya faru.
Ko An Ci Riba A Zanga-zangar?
Duk da irin tafka asarar da ake ganin wannan zanga-zanga ta haifar, akwa wadanda ke ganin an samu riba domin kuwa an kara samun hadin kai a tsakanin ‘yan kasa talakawa musamman yadda aka ga mabiya addinin Musulunci da na Kirista a garin Jos suna huldodi na ‘yan uwataka maimakon fadar addini.
Kiristoci sun tsare Musulmai lokacin da suke gudanar da Sallah a yayin gudanar da zanga-zangar a Jos.
Haka kuma, daga jin labarin shirin gudanar da zanga-zangar; gwamnatin tarayya ta dauki wasu matakai na shawo kan matsalar kuncin yaruwar da ake ciki, inda gwamnati ta aike da shinkafa tirela 20 ga kowace jiha tare da sanar da sayar wa ma’aikata shinkafa mai nauyin kilo 50 kan Naira 40,000 da dai sauran matakai masu alaka da wannan.
A yanzu haka kuma, mutane da dama sun koma ga Allah, wanda har wasu sun fara shelar fara alkunutu tare da gudanar da saukar Alkur’ani tare da yin azumi; domin samun shugabanci da shugabanni nagari a Nijeriya.