A yau Alhamis ne aka kaddamar da dandalin tattaunawar hadin gwiwar tattalin arziki na RCEP na shekarar 2022 a birnin Qingdao.Â
Yayin taron, shugaban hukumar inganta cinikayyar kasar Sin ya nuna cewa, RCEP, wata yarjejeniyar kulla dangantakar abokantakar tattalin arziki ce ta yanki, wadda ke amfani ga bunkasuwar kamfanoni a matsayin wata babbar yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci ta yankin a zamanance, cikakke, bisa inganci da kuma amfanar juna.
Yarjejeniyar RCEP ta fara aiki ne a ranar 1 ga Janairun bana, kuma a hukumance, tana alamta bude yankin cinikayya cikin ‘yanci mai kunshe da al’ummu mafi yawa, mafi girman ma’auni na tattalin arziki da ciniki, kana mafi girman damar ci gaba a duniya.
A tsakanin fiye da rabin shekara, adadin kasashen da suka amince da wannan yarjejeniya sun kai 13 a sassan duniya daban daban. (Mai fassarawa: Safiyah Ma daga CMG Hausa)