A kalla mambobin jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) dari bakwai, suka koma jam’iyyar Labour a jihar Adamawa.
Da take jawabi a madadin mutanen da suka canja shekar ranar Alhamis a Yola, Maryam Alhaji Sale, tace jam’iyyar Labour, itace jam’iyyar da zata fidda musu Kitse a wuta, don haka suka dawo jam’iyyar, daga jam’iyyarsu ta NNPP.
Da yake jawabin amsar mambobin jam’iyyar NNPP da suka canja shekar a Yola, dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar Labour a jihar Umar Mustapha (Otumba Ekiti), yace jam’iyyar ta shigo jihar da haskenta, saboda haka shi zai ceto jama’ar jihar a babban zaben 2023.
Ya ci gaba da cewa “tarihi zai maimaita kansa a Adamawa, domin kuwa jam’iyar za ta amshe ragamar mulki a hannun jam’iyyar PDP a babban zaben 2023.
“Jam’iyyar Labor za ta kafa gwamnatin kowa da kowa, babu banbancewa tsakanin kabila ko addini, za kuma ta farfado da tattalin arzikin jiha, jama’a za su yi farin ciki da gwamnatin Labour fati” inji Otumba.
Haka kuma dan takarar kujerar gwamnan ya yabawa jama’ar jihar, bisa karban jam’iyyar Labour a matsayin jam’iyyarsu, yace sauran jam’iyyu sun kadu da zuwan jam’iyyar Labour duba da kwarewa da kuma nasarorin da dan takarar kujerar shugaban kasar jam’iyyar Peter Obi, ke dashi.
Yace “Peter Obi, shine daya telo cikin gwamnoni, da a karshen wa’adin mulkinsa ya bar naira miliyan dubu 70, da dalar Amurka miliyan 150, a lalitar gwamnatin jihar Anambara.
“A daidai lokacin da gwamnoni suke gina manyan gidaje, Peter Obi, alummarsa ya gina, ba kansa ba, wannan itace manufar jam’iyyar Labour” inji Otumba.
Da shima ke jawabi shugaban jam’iyyar Labour ta jihar Mista Nicolas Christopher, yace zuwan jam’iyyar fata ce ga jama’ar jihar, wacce ta zo da nufin kafa ingantacciyar gwamnati a kasa da jihar Adamawa.