Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, a ranar Lahadin da ta gabata, ta bukaci gwamnatin tarayya da rundunar ‘yansandan Nijeriya da su gaggauta neman afuwarta, biyo bayan farmakin da jami’an tsaro suka kai a hedikwatarta da ke Abuja a daren Laraba.
An yi wannan kiran ne duk da bayanin da hukumar ‘yansandan suka yi cewa, ba ginin NLC suka yi nufin kai wa samame ba, sannan kuma sun bayyana dalilan kai samamen.
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Sojoji Sun Ƙona Motocin Sintiri 2 A Sakkwato
- Na Yi Alƙawarin Kawo Wa APC Kano A Zaɓen 2027 – Doguwa
Sai dai bayan wani taron gaggawa da kungiyar NLC ta gudanar a ranar Asabar din da ta gabata, kungiyar ta yi watsi da bayanin da ‘yansandan suka yi na kai samamen, inda tace, wani shiri ne da aka tsara domin a boye hakikanin dalilan da suka sa gwamnati ta dauki matakin kai wa ginin kungiyar samamen.
A cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya sanyawa hannu a Abuja, majalisar gudanarwar kungiyar (NEC) ta nuna matukar damuwarta game da samamen da aka kai mata a ranar 7 ga watan Agusta, jim kadan bayan wani muhimmin taro da aka yi na tattauna batun halin da mambobin kungiyar ke ciki biyo bayan zanga-zangar nuna adawa da kuncin rayuwa da ake fama da shi a fadin kasar.
NEC ta yi Allah-wadai da samamen inda ta bayyana shi a matsayin wani abu da ba a taba yin irinsa ba wanda ke barazana ga lafiyar ma’aikatan Nijeriya tare da tauye hakin kungiyoyin kwadago kamar yadda yarjejeniyar kungiyar kwadago ta duniya (ILO) da kundin tsarin mulkin Nijeriya suka tanada.