Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce cinikayya tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka ta bunkasa bisa daidaito, cikin watanni 7 na farkon shekarar bana.
Alkaluman da hukumar ta fitar na watannin Janairu zuwa Yulin bana, sun nuna karuwar kaso 5.5 bisa dari a cinikayyar sassan biyu, kan na shekarar da ta gabata, adadin da ya kai darajar kudin Sin yuan tiriliyan 1.19, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 166.6.
Kasar Sin ce babbar abokiyar cinikayyar kasashen Afirka cikin shekaru 15 a jere, kamar yadda hukumar kwastam ta Sin ta tabbatar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)