Donald Trump ya kara jaddada matsayarsa a kan kwararar baki cikin Amurka, inda ya sha alwashin aiwatar da manufarsa ta fatattakar baki ”mafi girma a tarihi”, idan ya sake zama shugaban kasa.
A hirar da ya yi kai tsaye da shugaban shafin sada zumunta na D, Elon Musk, Mr Trump ya yi karin haske kan matsayar sa game da baki masu shiga Amurka ba bisa ka’ida ba, da kuma yunkurin kashe shi da aka yi.
- Shugaban Seychelles: Raya Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Na Da Makoma Mai Haske
- Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu
An dan samu tsaiko kafin fara tattaunawar da dinbin jama’a suka yi ta jira domin sauraro a shafin X.
Shi dai Mr Elon Musk ya alakanta jinkirin da aka samu ne da yunkurin yin kutse da ya ce wasu sun rika yi cikin shafin, a daidai lokacin da ake shirin fara tattaunawar.
Dan takarar shugabancin Amurkan a jam’iyyar Republican, ya shaidawa hamshakin attajirin cewa ba zai yi wata-wata ba, wajen zartar da korar baki mafi girma a tarihi, idan har ya lashe zaben shugaban kasa a watan Nuwamba mai zuwa.
Mr Trump ya ce ba gudu babu ja da baya a shirin sa na gina katangar da za ta zamo shinge domin kare kasarsa daga kwararar bakin da za su zame mata barazana.
Ya ce: “Aikata laifi ya ragu a duniya baki daya, kuma ka jira tukun sai ka ga alkalumman da muke da su.
Wannan babban laifi ne, shiga kasa ba bisa ka’ida ba. Ya kara da cewa ”Mutane ne abin tsoro. Mutane ne da aka tura gidan yari saboda aikata kisan kai da sauran manyan laifuka, kuma sun zo suna turo mana su cikin kasarmu, suna kuma gargadin su cewa idan har suka koma za a kashe su.
Ko dai za a yanke masu hukuncin kisa ko kuma a kashe su nan take, idan har suka koma kasashen nasu. Wadan nan fa masu laifi ne da tsananin laifinsu ya sa muke kallon namu masu laifin kamar ba masu laifi ba, abin da suke aikatawa ya yi muni sosai.’’
An dai yi wannan tattaunawa ce bayan abokiyar hamayyar Donald Trump, Kamala Harris, ta shige gabansa a kuri’ar jin ra’ayin jama’a.
Mr Musk ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Mr Trump ne bayan an yi yunkurin kashe tsohon shugaban Amurkan a wajen yakin neman zabe a watan jiya.
A ranar Litinin Donald Trump ya koma amfani da shafin D, a karon farko cikin kusan shekara guda, kuma ya wallafa sakonni bidiyo na neman zabensa.