Wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram, ‘Awana Alhaji Mele Keremi’ da wasu ‘yan ta’adda tara sun mika wuya ga rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) da ke Cross Kauwa a jihar Borno.
A wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na rundunar MNJTF, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar, ya ce, Keremi, wanda ya kasance na hannun daman wani fitaccen kwamandan Boko Haram, ya bayyana cewa, yana da hannu a hare-haren ta’addanci da dama da suka kai a yankin Monguno zuwa Baga.
Hakazalika, sojojin na MNJTF sun kuma tarbi Babagoni Modu da wasu mutane takwas da suka yi nasarar tserewa daga sansanin ‘yan Boko Haram da ke Marte.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp