Dan kwallon kafar Jamus, Ilkay Gundogan, ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa kwallo.
Ilkay mai shekaru 33, ya kammala bugawa kasarsa wasa bayan ya buga wasanni 82, ya jefa kwallaye 19, da kuma taimakawa aka zura bakwai yayin da ya buga gasar cin kofin Turai na karshe a matsayin kyaftin.
Dan wasan Barcelona, Gundogan ya sanar da kawo karshen kwallonsa a tawagar kwallon kafa ta Jamus, bayan shafe shekaru 13 yana sanye da rigar kasar.
Dan wasan mai shekaru 33, ya kara da cewa abin da ya fi daukar hankali a rayuwarsa shi ne zama kyaftin a lokacin gasar cin kofin Turai da ta gabata bayan shekaru da yawa.
“A karshe na samu nasarar sake farantawa al’ummar kasar Jamus, na bayar da gudunmawata a matsayina na kyaftin yana sa ni farin ciki,” in ji shi.